Bayan Gama Duban Wata, Saudiyya Ta Sanar da Ranar Idin Karamar Sallah a 1445/2024
- Masarautar Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar Litinin, 29 ga watan Ramadan, 1445 wanda ya yi daidai da 8 ga watan Afrilu
- Sakamakon haka ta bayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal watau ranar idin ƙaramar sallah
- Hakan na nufin al'ummar musulmai a Saudiyya za su tashi da azumi na 30 gobe Talata kamar yadda addinin musulunci ya tanada
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Ƙasar Saudiya ta bayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afirlu, 2024 a matsayin ranar idin ƙaramar sallah (Eid-El-Fitr) ta shekarar 1445/2024.
Hakan ya biyo bayan rashin ganin jaririn watan Shawwal a yau Litinin, 29 ga watan Ramadan, 1445AH wanda ya zo daidai da 8 ga watan Afrilu, 2024.
Wannan na nufin watan Ramadan zai cika 30 a bana kuma ranar Laraba za ta kama 1 ga watan Shawwal, watau ranar hawa idin karamar sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatar da ke kula manyan masallatai biyu masu daraja, Inside The Haramain ce ta wallafa sakamakon duban jinjirin watan a shafin manhajar X watau Twitter.
Sanarwar ta ce:
"Ranar 10 ga watan Afrilu, 2204 za a yi Eid El Fitr saboda ba a ga jinjirin wata ba a ƙasar Saudiyya yau (Litinin, 29 ga watan Ramadan, 1445/8 ga watan Afrilu, 2024."
Yau za a duba wata a Najeriya
Idan baku manta ba, Sarkin musulmi kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ba da umarnin a fara duban wata yau Litinin.
Idan aka ga wata a Najeriya za a yi sallah ƙarama gobe Talata, idan kuma ba a gani ba kamar Saudiyya, to za a cika azumi 30 a wannan shekarar.
NiMet ta fitar da hasashe
A wani rahoton kuma hasashen hukumar NiMet ya nuna cewa za ayi zazzafar rana da kuma tsawa daga ranar Litinin zuwa Laraba a Nijeriya
Talata zuwa Laraba ne ake sa ran al'ummar Musulmin duniya, ciki har da na Nijeriya za su gudanar da bukukuwan Sallah
Asali: Legit.ng