Bukukuwan Sallah: NiMet Ta Yi Hasashen Za Ayi Zafin Rana da Tsawa Daga Litinin Zuwa Laraba

Bukukuwan Sallah: NiMet Ta Yi Hasashen Za Ayi Zafin Rana da Tsawa Daga Litinin Zuwa Laraba

  • Hasashen hukumar NiMet ya nuna cewa za ayi zazzafar rana da kuma tsawa daga ranar Litinin zuwa Laraba a Nijeriya
  • Talata zuwa Laraba ne ake sa ran al'ummar Musulmin duniya, ciki har da na Nijeriya za su gudanar da bukukuwan Sallah
  • Za a iya fuskantar iska mai karfi hade da ruwan sama da tsawa, lamarin da ya kamata jama'a su yi taka tsantsan," a cewar NiMet

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta yi hasashen zazzafar rana da kuma tsawa daga ranar Litinin zuwa Laraba.

NiMet ta yi hasashen hasken rana tare da tsawa na kwanaki 3 daga Litinin
Za a yi tsananin rana a ranakun bukukuwan Sallah a Nijeria, hukumar Nimet ta fitar da rahoto. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An fitar da hasashen yanayi na NiMet a ranar Lahadi a Abuja, wanda ya nuna za ayi zafin rana da lullumi a sassan jihohin Yobe da Borno a ranar Litinin, tare da yiwuwar tsawa a wani bangare na Kebbi.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

A cewar rahoton jaridar Premium Times, NiMet ta ce za a yi tsananin rana a sauran sassan Arewa tare da hadari a lokutan safiya zuwa kafin rana ta take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NiMEet: Hasashen yanayin ranar Litinin

“A yammacin ranar Litinin, ana sa ran za a yi tsawa a wasu sassan jihohin Bauchi, Taraba da Kaduna bayan haduwar hadari ko ma da saukar ruwa.
"Rana ba za ta yi zafi a yankin Arewa ta tsakiya ba inda kuma ake sa ran za a yi tsawa a sassan Neja, Kwara da Benuwai da safe.
“Har ila yau, ana sa ran za a yi tsawa a wasu sassan Filato, Abuja, Benuwai, Nasarawa da Kogi kafin lokacin da rana za ta fadi.”

- NiMet

NiMet: Hasashen yanayin ranar Talata

A ranar Talata, ana sa ran hadari zai mamaye samaniya a Arewacin Nijeriya tare da yiyuwar yin tsawa da safe a sassan jihohin Taraba da Adamawa.

Kara karanta wannan

Yaki da garkuwa da mutane: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 85 da ake zargin 'yan ta'adda ne

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa hukumar ta yi hasashen tsawa mai yawa a wasu sassan jihohin Taraba, Zamfara, Katsina, Kaduna da Bauchi.

Amma an yi hasashen cewa hadari zai iya lullube rana a yankin Arewa ta tsakiya yayin da ranar ta fara hudowa.

Amma idan rana ta take sosai, ana sa ran za a yi tsawa a wasu sassan babban birnin tarayya, Nasarawa, Kogi, Filato, da Benuwai.

NiMet: Hasashen yanayin ranar Laraba

Hukumar ta yi hasashen za a yi rana a yankin Arewa a ranar Laraba, inda za a iya samun tsawa a wasu sassan jihohin Zamfara, Kebbi, Taraba, Kaduna, Adamawa da Bauchi.

"Iska mai karfi na iya haduwa da ruwan sama a wuraren da ake iya samun tsawa, lamarin da ya kamata jama'a su yi taka tsantsan da shi.
"An shawarci ma'aikatan jirgin sama da su sami sabbin rahotannin yanayi daga NiMet domin tsara ayyukansu na tafiye-tafiye."

Kara karanta wannan

Mafita mafi sauki: Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su shawo kan karyewar Naira

- NiMet

Wannan duk yana cikin sanarwar NiMet, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito..

Gwamnati ta ba da hutun Sallah

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata da Laraba a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan karamar Sallah.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, tare da yi wa al'umar Musulmi fatan yin bukukuwan lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.