Yadda yanayi zai kasance cikin manyan birane a Najeriya

Yadda yanayi zai kasance cikin manyan birane a Najeriya

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya NiMet (Nigerian Meteorological Agency), ta yi hasashen gamewar gajimare wajen haduwar hadari da kuma yanayi na marka-marka a wasu sassa da dama cikin manyan biranen kasar nan a ranar Lahadi.

NiMet a ranar Asabar cikin reshen dake garin Abuja ta yi hasashen cewa, yanayi na lullumi da kuma haduwar hadari gami da yiwuwar saukar ruwan sama na marka-marka zai auku cikin wasu manyan da suka hadar da Filato, Mambila, Gombe, Nasarawa da kuma Yola a safiyar Lahadi.

Yadda yanayi zai kasance cikin manyan birane a Najeriya

Yadda yanayi zai kasance cikin manyan birane a Najeriya
Source: Depositphotos

Ta yi hasashen yiwuwar saukar ruwan sama da rana da kuma yammaci a biranen Abuja, Makurdi, Kaduna, Lokoja, Lafia da Neja a bisa ma'aunin zafi na celsius daga 37 zuwa 28 da kuma 27 zuwa 19.

Hukumar ta yi hasashen gamewar gajimare da kuma saukar ruwa sama a safiya da kuma gabanin rana tayi zawali a wasu manyan biranen Arewa da suka hadar da Nguru da Potiskum a bisa ma'aunin zafi na celsius daga 42 zuwa 35 da kuma 28 zuwa 24.

KARANTA KUMA: Sayen gidan sauro na $16m asara ce a Najeriya - Aisha Buhari

A hasashen hukumar NiMet, jihohin da ke Kudancin Najeriya za su mamakon ruwan sama yayin fuskantar yanayi na zafi a bisa ma'aunin celsius daga 33 zuwa 31 da safiya da kuma 24 zuwa 22 da Yammaci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel