An Runtuma Kora a Bankin CBN, Manyan Ma'aikata 40 Sun Rasa Aiki

An Runtuma Kora a Bankin CBN, Manyan Ma'aikata 40 Sun Rasa Aiki

  • Wasu ma'aikatan babban bankin Najeriys (CBN) da suka kai mutum 40 sun rasa aikinsu bayan bankin ya ba su takardun kora
  • Daga cikin waɗanda sabuwar korar ta ritsa da su akwai mataimakin darakta a CBN mai kula da sashen NCR
  • Sallamar ta su daga bakin aiki ta sanya adadin mutanen da aka kora daga CBN ya kai mutum 67 a ci gaba da garambawul ɗin da Olayemi Cardoso yake yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya sallami wasu ma’aikatansa a ci gaba da gyare-gyaren da ake yi a bankin.

Bankin na CBN ya kori ma’aikata 40 akasari daga sashen kuɗi na ci gaba (DFD), kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ka mayar da Pam matsayin shugaban NCPC": Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu

An kori ma'aikata a CBN
Ma'aikatan CBN 40 sun rasa aiki babban bankin Najeriya Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Waɗanne ma'aikata CBN ya kora?

Daga cikin waɗanda korar ta shafa akwai Musa Zgabawa Bulus, mataimakin darakta na CBN, mai kula da sashen bayanan bashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Korar dai ta shafi mataimakan daraktoci ne inda aka sallami 22 daga sashen DFD sai kuma sauran 18 daga sashen kula da lafiya, rahoton da jaridar Tribune ya tabbatar.

Idan dai ba a manta ba aƙalla ma’aikata 27 ne akasarinsu daraktoci a bankin, korar farko ta shafa, yayin da ake shirin ci gaba da sallamar wasu nan da ƴan kwanaki masu zuwa.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai daraktoci takwas, mataimakan daraktoci 10, ƙananan daraktoci biyar, manajoji biyu da manyan manajoji biyu.

A halin yanzu adadin ma’aikatan da abin ya shafa sun kai 67, a ci gaba da garambawul ɗin da Olayemi Cardoso yake yi a bankin.

Kara karanta wannan

Mafita mafi sauki: Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su shawo kan karyewar Naira

CBN ya karya farashin Dala

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya sake karya farashin Dala yayin da ya fara siyar da ita ga halastattun ƴan canji kan farashi mai arha.

Babban bankin ya tura wata takardar sanarwa ga ƴan canji (BDC), inda ya sanar da su cewa CBN ya siyar wa da kowane ɗaya daga cikinsu $10,000 kan farashi N1,251/$.

Bankin ya kuma umurci ƴan canjin da su sayar da Dala ga abokan cinikin da suka cancanci samunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel