Bikin Karamar Sallah: Tinubu Zai Shilla Zuwa Legas, Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Lokaci

Bikin Karamar Sallah: Tinubu Zai Shilla Zuwa Legas, Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Lokaci

  • Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai shilla Legas domin gudanar da bikin karamar Sallah
  • Al'ummar Musulmi a fadin duniya na gudanar da bikin karamar Sallah domin nuna farin ciki na kammala azumin watan Ramadana
  • Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale wanda ya fitar da sanarwar a ranar Asabar, ya ce ranar Lahadi Tinubu zai bar Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja, babban birnin Nijeriya a ranar Lahadi zuwa Legas domin gudanar da hutun bikin karamar Sallah.

Fadar shugaban kasa ta fadi lokacin da Tinubu zai tafi hutun Sallah
Shugaba Tinubu zai ci gaba da ayyukan ofis da zarar ya kammala hutun karamar Sallah. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Musulmi a fadin duniya na gudanar da bikin karamar Sallah ne bayan kammala azumin Ramadan na kwanaki 29 ko 30.

Kara karanta wannan

Lamunin karatu: Tsare-tsaren da gwamnati ta yi na fara ba dalibai rancen kudi

A cikin wata sanarwa daga Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Tinubu zai yi hutun bikin sallar ne tare da iyalansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai shilla Legas ranar Lahadi

Sanarwar wacce Dolusegun Dada, mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sada zumunta ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce:

"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa Legas a ranar Lahadi domin gudanar da bikin Eid-el-Fitr.
"Yayin da karamar Sallah ke nuna kammala azumin watan Ramadan, shugaban kasar tare da iyalansa za su gudanar da bikin ne ta hanyar yi wa Nijeriya addu'a."

Sanarwar ta kuma kara da cewa shugaban kasar zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na ofis da zarar ya kammala hutun bikin sallar.

Karanta sanarwar a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.