Kwankwaso Ya Soki Wasu Gwamnoni, Ya Faɗi Hanya 1 da Za Kawar da Ƴan Bindiga a Najeriya

Kwankwaso Ya Soki Wasu Gwamnoni, Ya Faɗi Hanya 1 da Za Kawar da Ƴan Bindiga a Najeriya

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce dakarun sojojin Najeriya za su iya magance matsalar tsaro idan suka samu abin da suke so
  • Kwankwaso, tsohon ministan tsaro ya ce jam'iyyar NNPP tana da tsarin yadda tsaro da kwanciyar hankali za su dawo idan ƴan Najeirya suka zaɓe ta
  • Ya faɗi haka ne yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin zartarwa na NNPP a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jagoran New Nigeria People’s Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce sojoji za su iya kawo karshen kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Kwankwaso ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya za ta iya kawar da wannan matsala ta tsaro gaba ɗaya matuƙar ta samu kwarin guiwar da ya dace, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

PDP da APC sun gaza, Kwankwaso ya fadi jam'iyyar da za ta yi wa 'yan Najeriya adalci

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.
Sojoji na iya kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi Najeriya, in ji Kwankwaso Hoto: KwankwasoRM
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Kwankwaso ya faɗi haka ne yayin da yake hira da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron kwamitin zartarwa na NNPP ta ƙasa a Abuja ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya faɗi mafita

Ya ce duk da cewa hakkin gwamnatin tarayya ne kawo ƙarshen matsalar tsaro, ‘yan Najeriya na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bada muhimman bayanai ga hukumomin tsaro.

Kwankwaso, tsohon ministan tsaro ya ce:

"A matsayina na tsohon ministan tsaro, tsohon babban jami’in tsaro na jihar Kano tsawon shekaru takwas, wanda ya san siyasa ciki da waje, na san cewa magance ƙalubalen tsaro ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya.
"Muna kallo wasu jihohi sun kafa rundunar su ta tsaro, wani lokacin abun kamar ka yi dariya, matakin da muke yanzu mataki ne na sojoji, duk wani abu da ya gaza haka ba zai yi aiki ba.

Kara karanta wannan

Dala ta yi muguwar faɗuwa, ta dawo ƙasa da N700 a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

"Kuma ya zama wajibi a kan kowane ɗan Najeriya a haɗa kai wuri ɗaya domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Mu da muka fito daga kauyen mun san yadda manoma ke zuwa gonakin su, amma yanzu ba za su iya ba."

NNPP za ta iya warware komai

Kwankwaso ya ce jam’iyyar NNPP tana da tsarin da za a bi wajen magance matsalolin tsaro da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta idan ‘yan Najeriya suka ba su dama.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ƙara da cewa NNPP ce kaɗai ta rage mafita ga ƴan Najeriya, yana mai cewa jam'iyyun APC da PDP sun gaza.

Yan sanda sun kama mutum 120

A wani rahoton kuma Dakarun ƴan sanda sun yi nasarar cafke mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar Kano a watan Maris

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daga cikin waɗanda aka kama har da masu garkuwa da mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262