Tsohon Gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso ya karyata rade-radin shirin komawa APC
- Rabiu Musa Kwankwaso ya musanya rade-radin cewa zai kuma sauya-sheka
- Wani hadimin tsohon gwaman ya ce jita-jitar da ke ta yawo ba gaskiya ba ne
- Sanata Kwankwaso ya dawo PDP kafin zaben 2019 bayan shekaru hudu a APC
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata rade-radin da su ke yawo na cewa ya na shirin sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran PDP a Kano, ya ce zancen cewa shi da magoya bayansa za su bar jam’iyyar ba gaskiya ba ne.
Jaridar nan ta Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021.
KU KARANTA: Kwankwaso ya kammala shirye-shiryen barin PDP, ya koma APC
Babu maganar a koma jam'iyyar APC mai mulki
Shugaban tafiyar na Kwankwasiyya ya nuna bai da wani buri na barin jam’iyyarsa ta PDP, ko ya koma APC, ko kuma ya kafa wata sabuwar jam’iyya kafin 2023.
Daya daga cikin hadiman tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya, Malam Saifullahi Hassan, ya tabbatar da wannan da manema labarai su ka nemi jin ta bakinsa.
Hassan ya shaida wa ‘yan jaridar cewa duk wata jita-jita da ake yi na cewa mai gidansa zai kuma sauya-sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP, zuki-ta-malle ce.
Legit.ng Hausa ta yi yunkurin jin ta bakin Saifullahi Hassan, amma ba ta iya samunsa ba tukuna.
KU KARANTA: Ni ba 'Dan jam'iyyar PDP ba ne inji Hadimin Atiku
Magoya bayan tsohon Ministan suna kukan cewa ba ayi wa mai gidansu adalci a tafiyar PDP, don haka aka fara bijiro da maganar ficewa daga jam’iyyar adawa.
Haka zalika wani hadimin shugaban PDP na jihar Kano, Shehu Wada Sagagi ya karyata rahoton. Sai dai har yanzu Rabiu Kwankwaso bai ce uffan da bakinsa ba.
Wani ‘dan Kwankwasiyya ya bayyana cewa APC za ta gyara kuskuren da tayi a baya idan ta dawo da Rabiu Kwankwaso, PDP kuma za ta gane ta yi babbar asara.
Zama a PDP sai wanda bai son ciwon kansa ba
Ganin abokin tafiyar Sanata Rabiu Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya fito yana sukar PDP. ya sa ake tunanin Kwankwasiyyar za ta tsere daga jam’iyyar adawa.
Idan za ku tuna, tsohon Mai magana da yawun bakin kwamitin neman zaben Atiku/PDP a zaben 2019, Buba Galadima ya yi kaca-kaca da PDP, ya ce ba ta da adalci.
Asali: Legit.ng