Kano: Ganduje Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da Abba Gida-Gida Ya Ɗauki Matakin Bincike
- Gwamnatin Kano, karkashin Abba Kabir Yusuf, ta kaddamar da kwamitocin shari'a da za su binciki ta'addancin da aka yi a siyasar 2023
- Haka zalika, kwamitin zai binciko yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta shude ta karkatar da kadarorin jihar
- Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa wannan binciken ba bita da kullin siyasa ba ne, illa dai yana so ya kwato wa al'umar Kano hakkokinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitocin shari'a guda biyu (JCIs) da za su binciki yadda aka karkatar da kadarorin gwamnati daga 2015 zuwa 2023.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa kwamitocin za su binciki tashin hankulan da aka samu da rahoton bacewar yara a lokacin zaben 2023.
"Za mu bi kadin jinin mutanenmu" - Abba
Gwamnan Yusuf ya ce bangar siyasa na zama koma baya ga dimokuraɗiyya, wacce ke kai ga asarar rayuka da dukiya, da kuma haddasa rikici tsakanin masu mulki da talakawansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce:
"Ba za mu kyale irin ta'addancin da aka yi a Kano da sunan siyasa ba, musamman a zaben 2023, ya zama wajibi mu gudanar da bincike a kai.
"Muna ba al'uma cewa za mu bi kadin jinin mutanen mu da aka zubar a lokacin zabe da bayansa. Ba za mu bari hakan ta sake faruwa ba."
Binciken ta'addanci a zaben Kano
Jaridar Leadership ta rahoto cewa kwamiti na farko wanda ke karkashin Mai shari'a Zuwaira Yusuf zai duba ayyukan ta'addanci da aka yi da bacewar mutane daga 2015 zuwa 2023.
Idan ba a manta ba, a zaben 2023, an zargi dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhasan Ado Doguwa, da kitsa kisan wasu magoya bayan NNPP a jihar.
"Muna so su gano wadanda suka aikata danyen aiki da wadanda suka dauki nauyin su, duk wani ta'addanci a zaben 2015, 2019 da 2023 a gano bakin zarensa domin yi wa tufkar hanci."
- A cewar Gwamna Yusuf.
Binciken shekaru 8 na mulkin Ganduje
Da yake kaddamar da kwamiti na biyu karkashin jagorancin Mai shari'a Faruk Lawan, Gwamna Yusuf ya ce su gano yadda aka karkatar da kadarorin jihar.
Ya ba su umarnin gano yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta shude ta karkatar da kadarorin gwamnati da ke a ciki ko wajen jihar.
Sai dai ya bayyana cewa wannan binciken ba wai bi ta da kullin siyasa bane, illa dai yana so ya cika alkawarin da ya daukar wa al'umma na yin adalci a ayyukansa.
Ganduje ya roki Abba ya koma APC
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Abdullahi Umar Ganduje ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da ya koma APC.
Ganduje wanda shi ne shugaban APC na kasa, ya ce jam'iyyarsu na da bukatar ƙarin gwamnoni wanda zai ba su damar shirya wa zaben 2027
Asali: Legit.ng