'Yan Sanda Sun Cafke Matasa Masu Yunkurin Kona Sansanin 'Yan Gudun Hijira a Jihar Arewa
- Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta samu nasarar cafke wasu matasa masu gurɓatacciyar zuciya da son aikata ta'asa
- Ƴan sandan sun cafke matasan ne bisa zarginsu da yunƙurin ƙona wani sansanin ƴan gudun hijira a jihar
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a birnin Maiduguri
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta kama wasu mutum huɗu da ake zargi da yunƙurin ƙona sansanin ƴan gudun hijira na Mafa da ke ƙaramar hukumar Mafa a jihar.
Mutanen da aka kama su ne Malum Usman mai shekara 16, Bulama Bukar mai shekara 14, Rawa Usman mai shekara 11 da kuma wanda ake zargi da ɗaukar nauyinsu, Babagana Umar, mai shekara 40, cewar rahoton jaridar The Punch.
A baya gwamnatin jihar wacce ta nuna damuwa kan yadda ake samun tashin gobara a sansanin ƴan gudun hijira, ta sha alwashin kama masu hannu a laifin tare da hukunta su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Lahadi, 31 ga watan Maris ne kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Farfesa Usman Tar, ya yi tsokaci kan lamarin, inda ya yi zargin cewa akwai hannun wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Yadda ƴan sanda suka cafke su
Sai dai, yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Maiduguri, ranar Alhamis, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, bai ambaci wata ƙungiya mai zaman kanta ba bisa ɗaukar nauyin lamarin.
A kalamansa:
"A ranar 24 ga watan Maris, 2024 da misalin ƙarfe 10:30 na safe, mafarautan Mafa sun je ofishin ƴan sanda na Mafa tare da wasu mutum uku dukkansu ƴan sansanin gudun hijira na Mafa waɗanda aka cafke su da ashana suna ƙoƙarin ƙona wani gida.
"Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutane ukun, wani Babagana Umar mai sayar da itace a unguwar garejin Muna a Maiduguri ya ɗauki nauyinsu inda ya basu kwangilar aikata wannan aika aika akan kuɗi naira 10,000."
Wanda ake zargi da ɗaukar nauyin, Umar, ya musanta ɗaukar nauyin matasan domin aikata laifin, rahoton Ripples Nigeria ya tabbatar.
Gobara ta tashi a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a cikin kasuwar Gamboru da ke birnin Maiduguri na jihar Borno.
Gobarar wacce ta tashin cikin dare dai ta shafi ɓangaren ƴan Katako tare da sauran wasu sassan kasuwar.
Asali: Legit.ng