Rayuka da Dama Sun Salwanta Bayan Wani Bam Ya Fashe a Jihar Arewa

Rayuka da Dama Sun Salwanta Bayan Wani Bam Ya Fashe a Jihar Arewa

  • An shiga jimami a jihar Taraba bayan wani abin fashewa da ake zargin bam ke ya salwantar da rayukan mutum huɗu
  • Wasu mutane da dama kuma sun samu raunuka bayan tashin bam ɗin a wani gida daga ƙauyen Gaita a jihar
  • Hakan na zuwa ne bayan an yi rikicin ƙabilanci a yankin wanda aka yi amfani da muggan makamai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Fashewar wani abu da ake zargin bam ne a cikin wani gida a jihar Taraba ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a ƙauyen Gaita da ke ƙaramar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Gwamna zai gwangwaje iyayen 'yar bautar kasa ta NYSC da katafaren gida, ya ambato dalilansa

Bam ya tashi a jihar Taraba
Wani bam ya salwantar da rayuka a Taraba Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter

Majiyoyi sun bayyana cewa fashewar ta kuma ta yi sanadiyyar jikkata mutane da dama ciki har da wani tsoho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Juma'a, 29 ga watan Maris 2024.

Wani mazaunin garin mai suna Musa ya ce mazauna ƙauyen sun ji wata ƙara daga wani gida a ƙauyen.

Ya ce mutanen ƙauyen sun gano cewa fashewar ta haifar da wani rami mai zurfi a cikin gidan inda wasu mutane huɗu da ake kyautata zaton ƴan gida ɗaya ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama.

Wani majiya a ƙauyen da ya so a sakaya sunansa, ya ce yankin ya fuskanci rikicin ƙabilanci wanda ya kai ga kashe mutane da dama, kuma ana zargin an yi amfani da makamai daban-daban da suka haɗa da bama-bamai a lokacin rikicin.

Kara karanta wannan

Abuja: Tashin hankali yayin da wani abu da ake zargin 'bam' ne ya tashi da mutane a watan azumi

Ba a samun damar jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Taraba ba, SP Usman Abdullahi, saboda yana kwance a asibiti a Jalingo.

An sace fasinjoji a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa fasinjoji da dama sun ɓace a wani harin da ƴan bindiga suka kai musu a jihar Taraba.

Fasinjojin waɗanda sun kai mutum 15 ciki har da mata da ƙananan yara an farmaki motarsu ne bayan ta taso daga jihar Benuwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel