Tashin Hankali Yayin da Ɗan Sanda Ya Mutu a Cikin Jirgi a Hanyar Zuwa Birnin Abuja

Tashin Hankali Yayin da Ɗan Sanda Ya Mutu a Cikin Jirgi a Hanyar Zuwa Birnin Abuja

  • Wani ɗan sanda da ba a gano sunansa ba ya mutu a cikin jirgin ƙasan da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu
  • An tattaro cewa ɗan sandan na ɗaya daga cikin dogaran jirgin waɗanda suke raka shi daga Kaduna zuwa Abuja
  • Wani fasinja ya bayyana cewa mamacin ya mutu ne bayan ya koka kan ciwon ƙirji ana cikin tafiya amma babu wani agajin gaggawa a jirgin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An shiga yanayin tashin hankali a jirgin ƙasan da ke jigilar fasinjoji tsakanin Kaduna zuwa Abuja yayin da wani jami'in ɗan sanda da ke rakiyar jirgin ya mutu ana cikin tafiya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke matasa masu yunkurin kona sansanin 'yan gudun hijira a jihar Arewa

Jirgin ƙasan na kan hanyar zuwa Abuja lokacin da jami'in ɗan sandan wanda ke aikin raka jirgin ya rasa rayuwarsa a kan hanya.

Jirgin kasan Kaduna-Abuja.
Dan sanda ya kamu da ciwon ƙirji ana cikin tafiya a jirgin ƙasa Hoto: @MrAbuSidiq
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ɗan sandan ya mutu

Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan ya bayyana cewa babu wata alamr ɗan sandan ba shi da lafiya a lokacin da jirgin ya taso daga tashar Kaduna.

Fasinjan ya ce marigayi ɗan sandan ya fara jin ciwo a ƙirjinsa kuma ya nemi mutane su taimaka masa ana cikin tafiya kafin daga bisani rai ya yi halinsa.

"Wani ɗan sanda, ɗaya daga cikin jami'an tsaron da ke raka jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya mutu yanzu ba daɗewa.Ya baro gida cikin ƙoshin lafiya.
"Amma ana cikin tafiya ya fara ciwon ƙirji, nan take ya nemi abokan aikinsa su ba shi magani da ruwa, babu ɗaukin gaggawa na kiwon lafiya a cikin jirgin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

"Kafin wani likita, wanda yana ɗaya daga cikin fasinjoji ya ƙaraso domin taimakawa ɗan sandan har rai ya yi halinsa," in ji mutumin.

A cewar Sahara Reporters, wani ganau ya yi zargin cewa ɗan sandan ya rasu ne bayan ciwon ƙirji ya kama shi kuma babu agajin kula da lafiya na gaggawa a jirgin.

Wata motar ƴan sanda ce ta zo ta ɗauki gawar mamacin bayan jirgin ya tsaya a tashar Kubwa da ke Abuja.

'Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja

A wani rahoton kuma yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi garkuwa da wasu biyu a yankin ƙaramar hukumar Bwari da ke birnin tarayya Abuja.

Wata majiya a rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa jami'ai sun matsa ƙaimi da nufin kamo maharan duk inda suka shiga suka ɓuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262