Gwamnan Arewa Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Magance Halin da Mutane Ke Ciki a Ramadan
- Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana mafita yayin da ake fama da matsananciyar yunwa musamman a watan Ramadan
- Abdullahi Sule ya ce duk da baya goyon bayan rabawa mutane abinci da kuɗi kyauta amma ya yarda cewa hakan ya zama wajibi a halin yanzu
- Gwamnan jihar Nasarawa ya jaddada cewa mafita ita ce bayan tallafin, ya kamata a lalubo hanyoyin da mutane za su dogara da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa ya zama tilas a tallafawa al'umma da kayan abinci a halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
Gwamna Sule ya ce duk da ba ya goyon bayan rabawa mutane kayan abinci kyauta da kuɗi, amma ya zama dole saboda mutane na fama da yunwa.
Abdullahi Sule ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels tv ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya jaddada muhimmancin magance matsalar yunwar da ake ciki tare da mai da hankali kan lalubo hanyoyin da mutane za su iya dogaro da kansu.
Gwamna Sule ya faɗi mafita
Ya ambaci koyar da sana'o'i da ba da jari ga waɗanda suka kammala karatun digiri da manoma domin su fara sana'o'i a matsayin hanyar ceto mutane.
Ya kuma bayyana shirin gwamnatinsa na hada hannu da cibiyoyi kamar Bankin masana’antu don samar wa matasa damarmaki, cewar rahoton Daily Trust.
Gwamna Sule ya jaddada cewa mafita ita ce a koya wa mutane yadda ake kamun kifi maimakon a ba su kifin kyauta, yana mai nanata bukatar dogaro da kai.
Sai dai kuma ya amince da wajabcin samar da kayan jin kai, musamman a lokutan da ake fama da matsananciyar yunwa kamar a watan Ramadan da ibadar kirista.
Idan baku manta ba, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi sun riƙa tsara shirin rabon kayan abinci ga mabuƙata da gajiyayyu domin rage masu radaɗi.
Sanata Natasha ta raba abinci kyauta
A wani rahoton kuma Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti, ta farantawa mutanen mazaɓarta yayin da ta raba tirelolin kayan abinci.
Natasha ta bayyana cewa ta yi haka ne saboda matsanancin matsin tattalin arzikin da mutane ke fama da shi a sassan ƙasar nan.
Asali: Legit.ng