Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki da Jiga Jigan APC, Ya Fadi Tanadin da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki da Jiga Jigan APC, Ya Fadi Tanadin da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin cewa ƴan Najeriya za su ga sauye-sauye masu ma'ana a watanni masu zuwa
  • A yayin da yake jawabi ga mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Tinubu ya ce ya ƙudiri aniyar ganin Najeriya ta samu ci gaba
  • Shugaban ya sake nanata cewa ya na yi wa Najeriya aiki tukuru domin ganin ya farantawa kowane ɗan ƙasa rai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi buɗa baki tare da mambobin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Shugaban ƙasan ya gaya musu cewa ƙoƙarinsu, sadaukar da kai da kuma aiki tukuru na iya sa Najeriya ta samu ci gaban da ake buƙata.

Kara karanta wannan

Bashin dalibai: Jerin mutum 5 da gwamnatin Tinubu ba za ta ba su rancen ba

Tinubu ya yi buda baki da jiga-jigan APC
Shugaba Tinubu ya yi buda tare da mambobin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na APC Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

Tinubu ya yi buɗa baki da jiga-jigan APC

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar a ɗakin taro na fadarsa da ke Aso Rock Villa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa shugaban ƙasan kan harkokin yaɗa labarai ɓangaren mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya sanya hotunan buɗa bakin a shafinsa na X.

Dada Olusegun ya sanya bayanin da shugaban ƙasan ya yi a wajen buɗa bakin a shafinsa na X.

A tare da Shugaba Tinubu a wajen buɗa bakin akwai mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Me Tinubu ya ce a wajen buɗa bakin?

Da yake jawabi a wajen buɗa bakin, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa:

"Aiki ne mai wahala da kuka yi wa al’ummar Najeriya alƙawarin samun sakamako mai kyau a lokacin da kuke yi min yaƙin neman zaɓe, dole ne in yi aiki kan hakan, babu wani siddabaru."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

"Na yi yaƙin neman zaɓe kan fata, dole ne na yi aiki kan wannan fatan, tare da aiki tuƙuru domin ganin wannan fatan ya zama abin farin ciki ga dukkaninmu."

Shugaban ƙasan ya ci gaba da cewa:

"Tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa, kada ku damu kan hakan. Eh mun san muna da ƙalubalen hauhawar farashin kayayyaki, hakan ba matsala ba ne, za mu saukar da shi ƙasa."
"Muna sake fasalin abubuwa, muna ƙara samun kuɗin shiga, sannan ƙimar mu ta fara dawowa a idon duniya."

Ayyukan da Tinubu zai kaddamar a Mayu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a birnin tarayya Abuja.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaban ƙasan zai ƙaddamar da ayyukan a watan Mayu domin cikarsa shekara ɗaya a kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng