An Shiga Jimami Yayin da Furodusa Kuma Darektan Fina-Finai Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Yayin da Furodusa Kuma Darektan Fina-Finai Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An tafka babban rashi bayan rasuwar shahararren furodusa kuma darektan fina-finan Nollywood, Frank Ogho Vaughan
  • Marigayin ya rasu ne a jiya Talata 2 ga watan Afrilu bayan ya sha fama da jinya a garin Warri da ke jihar Delta a Kudancin Najeriya
  • Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar darektoci ta DGN, Dakta Victor Okhai ya fitar a yau Laraba 3 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta – Fitaccen darekta kuma furodusan fina-finan Nollywood, Frank Igho Vaughan ya riga mu gidan gaskiya.

Vaughan ya rasu ne a garin Warri da ke jihar Delta a jiya Talata 2 ga watan Afrilu bayan ya sha fama da jinya.

Kara karanta wannan

Miyagu sun kutsa kai gidan dattijo mai shekaru 80, sun yi aajlinsa da matarsa a Arewa

Fitaccen furodusan fina-finai ya kwanta dama
Furodusa kuma darektan fina-finai a Nollywood, Frank Vaughan ya rasu. Hoto: Frank Igho Vaughan.
Asali: Facebook

Mukamin da marigayin ya riƙe a Nollywood

Marigayin Vaughan kafin rasuwarsa shi ne mataimakin shugaban kungiyar darektocin fim a Najeriya (DGN).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar DGN, Dakta Victor Okhai shi ya tabbatar da mutuwar darektan ga jaridar Vanguard.

“Tabbas ya rasu jiya, amma har yanzu ban samu cikakken bayani kan musabbabin mutuwar tasa ba.”

- Victor Okhai

Martanin kanin marigayin kan mutuwar Frank

Kanin marigayin, Philip Okpokoro wanda shi ma yake cikin harkar fina-finan ya tabbatar da mutuwar dan uwan nasa.

Vaughan ya yi fice wurin ba da umarni a fina-finai masu inganci inda ya taka muhimmiyar rawa wurin inganta masana’antar.

Marigayin daga bisani ya zama Fasto a cocin Dominion City da ke birnin Asaba na jihar Delta, cewar rahoton Leadership.

Har ila yau, Vaughan ya kasance mai fashin baki kan harkokin yau da kullum da kuma siyasa kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

InnaliLahi: Hadimin gwamnan APC ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 66

Dattijon da yafi dadewa a duniya ya rasu

A baya, mun ruwaito muku cewa dattijon da aka yi ittifakin yafi kowa dadewa a duniya ya riga mu gidan gaskiya.

Juan Vicente Perez Maro ya rasu ne a jiya Talata 2 ga watan Afrilu a kasar Venezuela ya na da shekaru 114 a duniya.

Kundin bajinta na Guinness a shekarar 2022 ya ba Maro lambar yabo na kasancewa wanda ya fi kowa daɗewa da kuma shekaru a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel