Lalacewar Wutar Lantarki: TCN Ta Yi Aiki Tukuru, Ta Gyara Matsalar Wuta da Aka Shiga a Najeriya
- A kwanakin nan ne aka samu lalacewar tushen wutar lantarki na Najeriya, 'yan kasa sun shiga tashin hankali
- Legit ta tattauna da mai sana'ar siyar da kankara, ta bayyana yadda daukewar wutar ya shafi sana'arta
- Ba wannan ne karon farko a 2024 ba da ake smaun lalacewar wutar lantarki a Najeriya, hakan ya faru a watannin baya
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya ce ya samu nasarar gyara wutar lantarkin kasar da ya lalace a kwanan nan.
Tushen wutan kasar da asali ake kula da shi a tsakiyar birnin Osogbo na jihar Osun ya ruguje ne a karo na biyu a shekarar 2024 da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 28 ga watan Maris.
A wata sanarwa a ranar Juma’a ta bakin Ndidi Mbah, kakakin TCN kamfanin ya ce an samu cikakkiyar damar maido da wutar da misalin karfe 10.00 na dare na ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka samu matsalar wuta
Da take bayanin yadda aka samu matsalar, ofishin kula da wutar lantarki ta lasa (NCC) ta ce an samu rugujewar tushen wutar ne sakamakon karancin gas.
A tun farko, 'yan Najeriya da dama sun shiga tashin hankali duba da yadda ake zafi ga kuma rashin samun wadatacciyar wutar lantarki.
A tattaunawar Legit Hausa da Amina Usman, wata mai sana'ar siyar da kayan sanyi a cikin watan Ramadana ta ce:
"Rashin wuta ya sa na tayar da janareta, ya cinye dan riban da nake samu. Tsadar mai ba zai bari ka iya cin komai ba.
"Dama wutar ne, ita ma din ba a kawo wa sai dare, to ka ga kwana biyu babu ita, gashi wasu daga kayayyaki na sun lalace, musamman kankarar fura da nono da nake yi. Bai son zafi."
Rashin wuta ya jawo tsadar kankara a Najeriya
A tun farko, 'yan Najeriya sun shiga matsala daidai lokacin da aka fara azumin watan Ramadana saboda rashin wuta.
Da dama sun koka kan cewa, ana tsadar kankara a kasar duba da yadda ake bukatarsa a wannan lokacin.
Legit ta yi magana da mutane da dama, sun bayyana yadda rashin wutar ya shafi rayuwar kasuwancinsu.
Asali: Legit.ng