Zargin Cushe a Kasafin Kudi: Akpabio Ya Fadi Hanyar da Ningi Zai Bi Domin a Dawo da Shi Majalisa

Zargin Cushe a Kasafin Kudi: Akpabio Ya Fadi Hanyar da Ningi Zai Bi Domin a Dawo da Shi Majalisa

  • Sanata Abdul Ningi da aka dakatar ya bayar da wa'adin mako ɗaya ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya mayar da shi bakin aiki
  • A martaninsa, Akpabio ya ce har yanzu bai samu takardar da Sanata Ningi ya aika ta hannun lauyansa Femi Falana SAN ba
  • Shugaban majalisar dattawan ya buƙaci Ningi da ya tuntuɓi takwarorinsa da ya zarga da laifin yin cushe a kasafin kuɗi sannan za a yi la’akari da yiwuwar ɗage dakatarwar da aka yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce har yanzu bai samu wata wasiƙa da Sanata Abdul Ningi ya aika masa da ita ba kan dakatarwar da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa 58 sun shiga uku saboda sun kyale an dakatar da Ningi a Majalisa

Sanata Ningi dai ta hannun lauyansa, Femi Falana ya bada wa’adin kwanaki bakwai ga Akpabio domin ya janye dakatarwar da aka yi masa.

Akpabio ya kare kansa kan dakatar da Ningi
Akpabio ya ba Sanata Abdl Ningi shawara Hoto: Godswill Obot Akpabio, Sen. Abdul Ahmed Ningi
Asali: Facebook

Shin Akpabio ne ya dakatar da Abdul Ningi?

Akpabio ya bayyana cewa matakin dakatar da ɗan majalisar shawara ce ta majalisar dattawa ba shi kaɗai ba, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga kalaman da lauyan sanatan, Femi Falana ya yi a baya game da wa’adin da aka ba shi na dawo da Ningi cikin majalisar.

Ya yi wannan jawabi ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja lokacin da ya dawo daga tafiya taron IPU da aka gudanar a Geneva.

A kwanakin baya ne majalisar dattawa ta dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda ikirarin cewa an yi cushen N3.7tr a kasafin kuɗin shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa na shirin ɗage dakatarwan da ta yi wa Sanata Abdul Ningi, ta faɗi dalili

Akpabio ya ba Sanata Ningi shawara

Da yake mayar da martani, Akpabio, a lokacin da ya dawo daga taron, ya ce har yanzu Sanata Ningi yana da damar da zai nemi afuwa wajen takwarorinsa da ya zarga da yin cushe a kasafin kuɗin.

Akpabio ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba majalisar dattawan za ta ɗage dakatarwar da aka yi wa Sanata Ningi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

An soki dakatar da Ningi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya da aka kafa domin kare muradun mutanen Arewacin Najeriya ta soki sanatocin da suka fito daga yankin.

Arewa Defence League ta yi Allah-wadai da yadda aka dakatar da Abdul Ahmed Ningi daga majalisar dattawa a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng