Kasurgumin Kwamandan Ƴan Ta'adda da Ya Fi Damun Mutane a Jihar Arewa Ya Miƙa Wuya

Kasurgumin Kwamandan Ƴan Ta'adda da Ya Fi Damun Mutane a Jihar Arewa Ya Miƙa Wuya

  • Wani babban kwamandan Boko Haram da ya jima yana addabar mutane a Gwoza da kewaye ya miƙa wuya ga sojoji a jihar Borno
  • Sarkin masarautar Gwoza, mai martaba Alhaji Mohammed Shehu Timta, ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Jumu'a
  • Basaraken ya bayyana cewa tuni aka mika tubabben kwamandan, Mallam Yathbalwe, ga rundunar sojoji domin ɗaukar mataki na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Babban kwamandan 'yan ta'addan Boko Haram, Mallam Yathbalwe, ya tuba ya mika wuya ga dakarun sojojin Operation Hadin Kai a jihar Borno.

Wannan kasurgumin ɗan ta'addan ƙungiyar Boko Haram ya jima yana aikata ta'addanci kan bayin Allah a yankin Gwoza da garuruwan da ke kewayen Tsaunin Mandara.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauko ɗan Arewa, ya naɗa shi a babban muƙami a watan azumi

Dakarun sojojin Najeriya.
Sarkin Gwoza ya tabbatar da mika wuyan kwamandan Boko Haram Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sarkin Gwoza da ke ƙaramar hukumar Gwoza a Borno, Mai martaba Alhaji Mohammed Shehu Timta, shi ne ya bayyana ci gaban ranar Jumu'a, cewar jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa Mallam Yathabalwe, kafin ya mika wuya, yana da hannu a kai hare-hare da kashe-kashe, ciki har da yi wa manoma yankan Rago a Gwoza da kewaye.

Wanene Mallam Yathbalwe a Boko Haram?

Rahoton Tribune ya nuna cewa yayin da Sarkin ke zantawa da ƴan jarida, ya ce:

"Muna farin cikin tabbatar maku da cewa babban kwamandan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo wanda ya dade yana addabar Gwoza da sauran kewayen tsaunin Mandara a yankina, Mallam Yathbalwe ya mika wuya.
"Bisa ra'ayin kansa ya fito daga wurin ɓuya da safiyar Juma’a ɗauke da bindigogi kirar AK47 guda biyu da wasu alburusai, ya miƙa wuya da sojojin 'Operation Hadin Kai' a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Babu hannu na a kashe sojojin Najeriya, Sarkin Delta da ya mika kansa ga 'yan sanda

"Daga nan ne aka mika shi ga dakarun sojin Najeriya da ke Gwoza, kuma za a wuce da shi Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin ci gaba da yi masa tambayoyi ko daukar mataki.
"Yathabalwe, kafin ya mika wuya, ya shafe shekaru da yawa yana aikata ta'addanci kan jama'ata, musamman manoman da ya hana zuwa gonakinsu. Muna fatan zaman lafiya ya dawo."

- Alhaji Mohammed Shehu Timta.

An daina satar ɗalibai a Borno

A wani rahoton kuma Gwamna Zulum ya bayyana dalilin da ya sa aka jima ba a ji ƴan ta'adda sun sace dalibai daga makarantu a jihar Borno ba.

Farfesa Babagana Zulum ya ce shirin samar da aminci a makarantu da suka kaddamar shekaru 7 zuwa 8 da suka wuce ya yi aiki yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262