Tinubu @72: Abin da Buhari Ya Fadawa Bola Bayan Ya Kira Shi Musamman a Waya
- Yayin da Shugaba Tinubu ya ke cika shekaru 72 a yau Juma'a 29 ga watan Maris, Muhammadu Buhari ya kuma taya shi murna
- Tsohon shugaban kasar ya kira Tinubu na musamman a waya domin sake jaddada masa goyon bayansa wurin inganta kasar Najeriya
- Wannan na zuwa ne bayan tsohon shugaban kasa, Buhari ya tura sakon murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jiya Alhamis 28 ga watan Maris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake taya Shugaba Tinubu murnar cika shekaru 72 a duniya.
Buhari ya sake taya shi murna bayan kiran waya da ya yi masa ta musamman domin bikin ranar haihuwarsa.
Abin da Buhari ya fadawa Tinubu a waya
Kakakin tsohon shugaban kasar, Garba Shehu shi ya bayyana haka a shafin X a yammacin yau Juma'a 29 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garba Shehu ya ce Buhari ya bayyana himmatuwarsa wurin ba Tinubu goyon baya dari bisa dari.
Har ila yau, tsohon shugaban ya jaddada aniyarsa wurin goyon bayan jam'iyyar APC karkashin Shugaba Tinubu domin ci gaba da inganta kasar.
Buhari ya kora addu'o'i ga Tinubu
Ya kora masa ruwan addu'o'i inda ya ce ya na da matukar muhimmanci yi wa shugabanni addu'a a kasa irin Najeriya.
Ya kara da cewa dacewar shugaban shi zai inganta Najeriya wurin inganta jama'ar kasar baki daya.
Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya cika shekaru 72 a duniya a yau Juma'a 29 ga watan Maris.
Manyan kasar da dama sun taya shi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa inda suka yi hada masa da addu'o'i.
Buhari ya yabawa Tinubu da ayyukan alheri
A baya, mun ruwaito muku cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan inganta kasa.
Buhari ya yi yabon ne yayin da ya ke ta ya shugaban murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jiya Alhamis 28 ga watan Maris.
A yau Juma'a ne 29 ga watan Maris ya cika shekaru 72 a duniya inda manya-manyan kasar suka ta ya murnar.
Asali: Legit.ng