Okuama: Sarkin da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Koma Hannun Sojoji, Ƴan Sanda Sun Yi Magana

Okuama: Sarkin da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Koma Hannun Sojoji, Ƴan Sanda Sun Yi Magana

  • Yan sanda sun miƙa Sarkin Ewu, Clement Ikolo, ga rundunar sojoji bayan ya miƙa kansa da yammacin ranar Alhamis
  • Basaraken na ɗaya daga cikin mutum 8 da hedkwatar tsaron Najeriya take nema kan zargin hannu a kisan gillan da aka yi wa sojoji 17 a Okuama
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da wannan ci gaban ga manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Rahotannin da suka fito a ɗazu sun nuna cewa Sarkin Ewu, Clement Ikolo, wnada ake nema ruwa a jallo kan kisan sojoji a Delta ya mika kansa ga ƴan sanda.

Sai dai a halin yanzun rundunar ƴan sanda ta miƙa fitaccen basaraken ga rundunar sojojin Najeriya domin ɗaukar mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Babu hannu na a kashe sojojin Najeriya, Sarkin Delta da ya mika kansa ga 'yan sanda

Sarki Clement Ikolo da sojoji.
Sarki Ikolo ya koma hannun sojojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army, urhobotoday
Asali: Facebook

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Delta, Bright Edafe, ne ya tabbatar da cewa Sarkin ya koma hannun sojoji, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Sarkin Ewu ya miƙa kansa?

Sarki Ikolo na ɗaya daga cikin mutane takwas da hedkwatar tsaron Najeriya ta ayyana tana nema ruwa a jallo bisa zargin suna da hannu a kisan sojoji 17 a kauyen Okuama.

Awanni bayan DHQ ta ce tana nemansu, basaraken ya miƙa kansa ga ƴan sanda a hedkwatar ƴan sanda ta jihar Delta ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2024, in ji Tribune Nigeria.

An ce sarkin ya isa hedkwatar ‘yan sandan jihar ne da misalin karfe 6:41 na yamma, domin miƙa kansa ga kwamishinan ‘yan sanda Olufemi Abaniwonda.

Kafin ya mika kan sa ga ‘yan sanda, sarkin ya yi magana da ‘yan jarida, inda ya nanata cewa ba shi da laifi, babu hannunsa a abin da ya faru a Okuama.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar mutum 313 da ake zargi da aikata ta'addanci

DHQ ta bayyana sunayen mutum 8

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hedkwatar tsaro ta bayyana wasu mutane 8 da suka hada da Ikolo da ake nema ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu wajen kashe jami’an soji 17.

Wadanda ake nema ruwa a jallo sun hada da Farfesa Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbo (Aka Amagben), da Akata Malawa David.

Sauran sune, Sinclear Oliki, wani basaraken gargajiya, Clement Ikolo Oghenerukeywe, Reuben Baru, da kuma Igoli Ebi.

Tinubu ya yi wa iyalan sojojin alƙawari

A wani rahoton kuma kun ji cewa Shugaba Tinubu halarci jana'izar sojojin da aka yi wa kisan gilla a ƙauyen Okuama, jihar Delta a ranar Laraba, 27 ga watan Maris

A wajen jana’izar jami’an da aka yi a Abuja, shugaban ƙasan ya yi wasu muhimman alƙawura ga iyalan sojojin da aka kashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262