Ana Daf Da Buda Baki, Buhari Ya Tura Sako Ga Tinubu, Ya Yi Masa Ruwan Addu'o'i
- Yayin da Shugaba Bola Tinubu ke cika shekaru 72 a duniya, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya shi murna
- Tsohon shugaban ya taya Tinubu murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa inda ya masa addu'ar samun tsawon rai
- Buhari ya ce tabbas magajinsa ya dakile matsaloli kasar da dama inda ya masa fatan karin lafiya domin inganta Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murnar cika shekaru 72.
Buhari ya yi masa fatan samun karin lafiya da nisan kwana domin 'yan Najeriya su amfana da salon mulkinsa.
Sakon da Buhari ya turawa Shugaba Tinubu
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar a shafin Twitter a yau Alhamis 28 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya yabawa Shugaba Tinubu kan yadda ya shawo kan matsalolin kasar.
Buhari ya yi masa fatan nasara a cikin mulkinsa inda ya roki ubangiji ya kara masa kwazo wurin inganta Najeriya.
Tinubu: Jawabin Buhari ta bakin Garba Shehu
"Da ni da iyalaina muna taya ka murnar cika shekaru 72 a duniya da lafiya."
"Muna maka fatan alheri da kuma nisan kwana mai dorewa domin ci gaba da inganta kasar Najeriya."
- Garba Shehu
Tinubu ya taya Aisha Buhari murna
A wani labarin mai kama da wannan, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tura sakon murna ga matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Tinubu ya tura sakon ne don taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarta shekaru 53.
Shugaban ya ce tabbas Aisha ta kasance mace ta daban wacce ta sadaukar da rayuwarsu wurin ayyukan alheri da za su inganta kasa.
Buhari ya jajantawa hadiminsa
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon jaje ga hadiminsa, Sunday Aghaeze kan rasuwar matarsa.
Buhari ya jajantawa hadiminsa a bangaren daukar hoto, bayan matarsa mai suna Mabel ta rasu a farkon wannan wata.
Tsohon shugaban kasar ya ce tabbas iyalan Aghaeze sun tafka babban rashin mata kuma uwa mai son jama'a da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng