Tinubu Ya Kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin Shugaban Kasa, an Samu Bayanai
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saka sunayen Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu da wasu 'yan kasuwa a kwamitin tattalin arziki
- Rahoto ya bayyana cewa Tinubu ya kaddamar da kwamitoci guda biyu da za su taimakawa gwamnati wajen farfaɗo da tattalin arziki
- Kwamitocin su ne kwamitin kula da tattalin arziki na shugaban kasa (PECC) da kwamitin agajin gaggawa na tattalin arziki (EET)
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa majalisar kula da tattalin arziki ta shugaban kasa (PECC) da kwamitin agajin gaggawa na tattalin arziki (EET).
Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale a cikin wata sanarwa ya ce bangarorin biyu za su taimakawa gwamnati wajen farfaɗo da tattalin arziki da bunkasa shi.
Tattalin arziki: Sunayen 'yan kwamitin PECC
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar PECC ta na da shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaba, sai Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran mambobi sun hada da shugaban majalisar dattawa, a matsayin shugaba, kungiyar gwamnoni, ministan kuɗi da tattalin arziki, gwamnan CBN da wasu ministoci.
Haka zalika, akwai wasu yan kasuwa da aka saka su a matsayin mambobi a majalisar domin yin aiki na tsawon shekara daya.
Sun hada da, Alhaji Aliko Dangote, Mr. Tony Elumelu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Ms. Amina Maina, Mr. Begun Ajayi-Kadir da sauran su.
Tattalin arziki: Sunayen 'yan kwamitin EET
Kwamitin EET kuwa, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito an dora masa alhakin samar da matakan gaggawa na farfaɗo da tattalin arziki, kuma yana karkashin jagorancin ministan kudi da tattalin arziki.
Mambobin kwamitin sun hada da gwamnan CBN, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, kungiyar gwamnoni, gwamnonin jihohin Anambra, Ogun da Neja.
Sauran sun hada da shugaban hukumar tattara haraji ta kasa, daraktan kasafi na tarayya, GCEO NNPCL, daraktan kungiyar tattalin arziki ta NECS, da mai ba shugaban kasa shawara kan makamashi.
Tsarin aikin kwamitin EET
Ana sa ran kwamitin EET zai gabatar da rahoton tsarin da za a bi wajen farfaɗo da tattalin arziki a 2024, wanda zai shafi watanni shida na shekarar.
Sanarwar Ngelale ta kuma yi nuni da cewa shugaban EMT, ministan kuɗi na da ikon gayyatar kowanne ministan kasar ko shugaban hukuma a kan abin da ya shafi wannan aiki.
A cewarsa, kwamitin EET zai dukufa a cikin watanni shida na gaba wajen ganin ya samar da mafita kan matsalar tattalin arziki, kuma zai ba majalisar PECC rahoton bincikensa.
Tinubu ya gana da Dangote, BUA
A wani labarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da manyan 'yan kasuwar da ake bi da su da suka hada Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu BUA da Tony Elumelu.
Legit Hausa ta ruwaito cewa ganawar ta shafi batutuwan tattalin arziki da yadda 'yan kasuwar za su taimaka wa gwamnati wajen magance matsalolin tattali da take fuskanta.
Asali: Legit.ng