Yayin da Tinubu Ya Halarci Jana’izar Sojoji, Hadiminsa Ya Soki Buhari Kan Rashin Kulawa
- Yayin da Shugaba Tinubu ya halarci jana’izar sojojin da aka kashe a Delta, hadimin Tinubu ya soki tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- Bayo Onanuga ya bayyana cewa a cikin shekaru 10 wannan shi ne karon farko da shugaban Najeriya ke halartar irin wannan taro a kasar
- Onanuga ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Laraba 27 ga watan Maris wanda mutane da dama suka kushe shi kan haka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Hadimin Shugaba Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya yi magana kan halartar jana’izar da shugaban ya yi a Abuja.
Onanuga bai tsaya nan ba, ya soki tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda kin halartar jana’izar sojoji da suka mutu a bakin aiki.
Sanarwa kan halartar jana'iza na Tinubu
Hadimin shugaban ya bayyana haka ne a yau Laraba 27 ga watan Maris a shafinsa na X yayin sanar da halaratar jana’izar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan shi ne karon farko a cikin shekaru 10 da shugaban Najeriya zai halarci irin wannan jana’iza ga sojojin kasar.
“Karon farko kenan a Najeriya cikin shekaru 10 da wani shugaba zai halarci taro irin wannan domin karrama sojojinmu.”
“Mun fada muku a wancan lokaci, Tinubu ya damu kwarai da kasar, yanzu ga shi ya na nunawa.”
- Bayo Onanuga
Buhari bai halarci jana'izar sojoji ba
A watan Nuwambar 2018, sojoji da dama sun mutu, hafsan sojin a wancan lokaci, Ibrahim Attahitu ya rasu a hadarin jirgin sama amma Buhari bai halarci jana’izarsu ba.
Sai dai wannan magana ta hadimin ta jawo cece-kuce a kafofin sadarwa inda wasu suka caccake shi kan saka siyasa a lamarin.
Mutane da dama sun soki Onanuga kan rashin daraja sojojin da suka mutu a bakin aiki inda ya ke maganar siyasa a dai-dai wannan lokaci.
Tinubu ya ba dattawan Okuama umarni
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci dattawa da sarakunan Okuama da su zakulo wadanda suka hallaka sojoji a jihar Delta.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya halarci jana’izar binne sojojin da aka yi ajalinsu a jihar Delta.
Asali: Legit.ng