Gumi Ya Amsa Gayyata, Ya Bayyana Abin da Ya Tattauna da Jami'an Tsaro Kan Ƴan Bindiga
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana tattaunawar da ya yi da jami'an tsaro bayan ya amsa gayyatar da suka yi masa
- Ranar Litinin, Ministan yaɗa labarai na wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ya ce hukumomin tsaro sun gayyaci malamin domin amsa tambayoyi
- Dakta Gumi ya ce tattaunawar da suka yi ta yi kyau kuma ya gode wa masu fatan alheri da suka nuna damuwa kan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Dakta Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa ya tattauna da jami'an tsaro bayan gayyatar da aka masa.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce sun yi tattaunawa mai ban sha'awa da jami'an tsaro, inda ya ce mara laifi ne kaɗai ya fi ƙarfin doka.
Malamin ya bayyana haka ne a wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan ya amsa gayyatar da hukumomin tsaron Najeriya suka yi masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba, bayan taron majalisar zartarwar ranar Litinin, ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce hukumomin tsaro sun gayyaci malam Gumi.
Ministan ya ce an gayyaci shararren malamin ne domin amsa wasu tambayoyi kan kalaman da yake yi game da ƴan bindiga, inda ya ce babu wanda ya fi karfin doka.
Abin da Gumi ya tattauna da mahukunta
Da yake ƙarin bayani
kan abin da suka tattauna, babban malamin musuluncin mazaunin Kaduna ya ce babu wani abun damuwa domin tattaunawarsa da jami'an tsaro ta yi kyau."Jiya da daddare na samu kiraye-kirayen waya da dama daga masu fatan alheri da ƴan jarida game da labarin cewa jami'an tsaro sun mun tambayoyi, babu wani abun damuwa.
"Eh, mun yi tattaunawa mai kyau ta yadda za mu kawo karshen ƴan bindiga kamar yadda kowa ke ƙoƙari a ɓangarensa don magance matsalar da ta addabi ƙasar nan. Babu gaba a tsakaninmu sai ladabi da girmamawa.
"Akwai bukatar dukkanmu mu haɗa kai a matsayin ƙasa mu yi aiki tare domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Na gode da nuna kulawarku, Allah ya ƙara tsare mu daga dukkan wani sharri."
- Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
Sojoji sun wanke waɗanda ake zargi
A wani rahoton na daban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta shirya za ta saki sama da mutane 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da ƙungiyar ƴan ta'adda.
Dakarun sojoji sun kama waɗannan mutanen ne a lokacin da ayyukan ƴan tada kayar baya ke cin kasuwa a Arewa maso Gabas.
Asali: Legit.ng