Gidajen Mai Sun Kara Kudi, Jihohi 10 a Najeriya Sun Sha Tsadar Man Fetur a Watan Faburairu
- Sabbin bayanai da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar sun nuna cewa ‘yan Najeriya sun sake shiga tsadar man fetur a watan Fabrairun 2023
- Bayanai sun nuna cewa, farashin litar man fetur ya karu da 157.57% a watan Faburairun 2024 idan aka kwatanta da watan na Faburairu a 2023
- Farashin mai mafi tsada a watan Fabrairu ya kasance ne a jihar Zamfara, sai jihohin Kebbi da Taraba, kamar yadda rahoton ya fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Hukumar Kididdiga ta kasa ta ce matsakaicin farashin lita daya na man fetur ya karu zuwa Naira 679.36 kan kowace lita a watan Faburairun da ta gabata.
Wannan yana nuna karuwar 157.57% idan aka kwatanta da N263.76 na farashin lita daya da aka siyar a watan Fabrairun 2023.
Idan aka kwatanta da farashin mai na watan Janairun 2024 na N668.30 da farashin Fabrairun 2024, an samu karuwar 1.66%.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NBS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta na Watch Price Watch da ta wallafa a shafinta na yanar gizo wanda Legit.ng ta samu.
Farashin mai a watan Yulin 2023 a wasu jihohi
Hukumar NBS ta yi bayanin yadda a wasu jihohin farashin mai ya tashi da kuma yadda ya sauka a wasu jihohin.
Jihar Zamfara ce ta kasance mafi ganin tashin farashin man fetur akan Naira 750.43, sai jihohin Kebbi da Taraba, da suka ga farashin N746.67 da N710.56, bi da bi.
A bangare guda, jihohin Kwara, Ogun da Benue sun kasance mafi ganin arahar farashin man fetur akan kudi N650.00, 650.83 da 652.73 bi da bi.
Jihohin da suka fi shan tsadar man fetur a Faburairun 2024
- Zamfara: N750.43
- Kebbi: N746.67
- Taraba: N710.56
- Gombe: N710.00
- Imo: N705.51
- Jigawa: N696.43
- Abia: N688.62
- Bauchi: N688.57
- Enugu: N688.21
- Yobe: N688.20
Matatar Fatakwal za ta fara aiki nan kusa
A wani labarin, shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce nan da mako biyu matatar mai ta Fatakwal, da ke jihar Rivers za ta fara aiki.
Kyari ya ce ya zuwa yanzu matatar ta karbi ganga 450,000 na danyen mai domin tacewa bayan da aka kammala gyaran matatar a Disambar 2023.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kyari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kwamitin majalisar dattawa da ke bincike kan yadda ake kula da matatun mai (TAM) na kasar.
Asali: Legit.ng