Kebbi: Barayin Shinkafa Sun Farmaki Hukumar Kwastam, Sun Tafka Mummunan Barna
- Matasa da ake zargin barayin shinkafa ne sun farmaki ofishin hukumar Kwastam a jihar Kebbi inda suka tafka barna
- Hukumar da ke yankin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa maharan sun sace buhunnan shinkafa akalla 29 daga cikin 40
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar a yankin, Mohammed Tajudden Salisu ya fitar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi – Wasu da ake zargin barayin shinkafa ne sun kai hari ofishin hukumar Kwastam da ke Yauri a jihar Kebbi.
Matasan sun farmaki ofishin tare da sace buhunan shinkafa 29 daga cikin 40 da hukumar ta kwace tare da dauke bingiga kirar AK-47.
Yadda aka kai hari kan hukumar Kwastam
Kakakin hukumar a yankin, Mohammed Tajudden Salisu shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Salisu ya ce wani daga cikin jami’an hukumar ya samu rauni yayin harin inda ya ce an yi nasarar kwato bindigar kirar AK-47.
“Hukumar ta yi nasarar kwace shinkafa buhuna 40 inda muka adana ta a ofishin da ke Yauri.”
“Bayan wani lokaci, matasa da ake zargin barayin shinkafa ne sun farmaki ofishin tare da tafka mummunana barna.”
- Salisu Tajudden
Barnar da barayin suka yi wa Kwastam
Tajudden ya ce yayin da suka ankara da zuwan matasan, sun tuntubi hukumomin tsaro da ke kusa da su domin kawo musu dauki, cewar Daily Trust.
Ya kara da cewa maharan sun lalata motar hukumar tare da wasu kayayyaki da suka hada da kujeru da kofofi da tagogi dan sauran abubuwa masu amfani.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumar ta bude iyakar Kamba da ke jihar domin inganta harkokin kasuwanci a yankin.
Tinubu ya ba hukumar Kwastam sabon umarni
A baya, mun ruwaito muku cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba hukumar Kwastam sabon umarnin kan abinci da suke kwacewa.
Tinubu ya umarci hukumar da su mayar da abincin da suka kwace daga ‘yan kasuwa domin siyar da shi.
Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke ci gaba da kwace kayan abinci da ake fita da su kasashen ketare ba bisa ka’ida ba.
Asali: Legit.ng