'Ƴan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wasu Mutum 20, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Watan Azumi

'Ƴan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wasu Mutum 20, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Watan Azumi

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari kan bayin Allah suna tsaka da cin kasuwa a yankin ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe mutum 21, ciki har da magajin garin sannan sun sace mutane da dama
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Neja, Wasi'u Abiodun, ya ce har yanzu bai gama tattara bayanai game da harin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Neja - Wasu ƴan bindiga sun halaka mutum 21 ciki har da magajin gari a kauyen Madaka da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da adadi mai yawa na mutane, waɗanda har yanzu ba a tantance yawansu ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe sabon ango a harin kasuwar Arewa, an samu karin bayani

Gwamna Umar Bago.
An kashe mutum 21 a jihar Neja Hoto: Muhammed Umar Bago
Asali: Facebook

Sun bayyana cewa maharan sun kutsa kai cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 3:00 na tsakar rana a ranar Alhamis, daidai lokacin da kasuwar kauyen ta cika maƙil.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar sun kuma kona gidaje da shaguna kusan 50, da kuma motoci da babura da dama yayin wannan mummunan harin.

Yadda ƴan bindiga suka yi ɓarna

Sun ce ‘yan bindigar dauke da muggan makamai sun shiga kauyen kana suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su fara kashe-kashe da ƙone-ƙone.

Wani mazaunin kauyen ya ce saboda babu jami'an tsaro a kauyen shiyasa ƴan bindigan suke shiga suyi abin da ransu ya so babu mai ɗaga masu yatsa.

Hakimin yankin, Isah Bawale, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Minna, babban birnin jihar, a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko da sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a watan Azumi

An tattaro cewa shekara ɗaya da ya gabata, ƴan bindiga sun kai farmaki wannan kauyen kuma sun kashe magajin garin.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce yana ci gaba da kokarin tantance rahotannin abin da ya faru a harin.

Kwamishinan tsaro na jihar, Bello Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce gwamnati na kokarin tsare dukkan garuruwan da ke noma a jihar, in ji rahoton Channels tv.

Wani mazaunin Madaka da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa adadin mutanen da suka mutu sun karu da safiyar Jumu'a.

Mutumin wanda ya nuna damuwa kan barnar miliyoyin da ƴan bindiga suka masu, ya ce an yi jana'izar mamatan yayin da ake ci gaba da neman waɗanda suka ɓata.

"Ba mutum 20 suka kashe ba, zuwa yau da safe (Jumu'a) mutane 30 muka yi wa sutura kuma har yanzun ana bincike."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar gwamnati a watan azumi, sun tafka ɓarna a jihar Katsina

"Ba karamar ɓarana suka yi ba, sun ƙona babura, shaguna da gidaje, ga shi lokacin kasuwa na tsaka da ci, muna rokon gwamnati ta kawo mana agaji," in ji shi.

Ƴan bindiga sun sace fasinjojin KTSTA

A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun tare motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 mallakin hukumar sufuri ta jihar Katsina, sun yi garkuwa da mutane da yawa.

Ganau sun bayyana cewa maharan sun tare motar ne a yankin ƙaramar hukumar Kankara ranar Alhamis, 2 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262