Gwamnan Katsina Ya Fadi Abin da Ya Kamata Al'ummar Jihar Su Yi Domin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Gwamnan Katsina Ya Fadi Abin da Ya Kamata Al'ummar Jihar Su Yi Domin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda na son ganin matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar jihar ta zama tarihi
  • Dikko ya buƙaci al'ummar jihar da su sanya jami'an rundunar tsaron jihar ta KCWC cikin adduo'insu domin su kawo ƙarshen ƴan binɗiga
  • Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ayyukan alherin da gwamnatinsa ta fara domin inganta rayuwar mutanen jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al’ummar musulmi da su ƙara kaimi wajen addu’o’i a lokacin azumin watan Ramadan.

Gwamnan ya buƙaci su sanya rundunar tsaron jihar ta KCWC cikin addu'a domin fatattakar ƴan bindiga a ƙananan hukumomin da ake fama da matsalarsu, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Dikko Radda: Gwamnan Katsina da ya ce ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba

Gwamna Radda ya bukaci a sanya jami'an tsaro a addu'a
Gwamna Dikko Radda na son kawo karshen 'yan bindiga Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wajen rabon hatsi ga mutane 2,000 da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Katsina ta tsakiya a majalisar wakilai, Danlami Musa ya ɗauki nauyinsa a tsohon gidan gwamnatin jihar da ke Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Dikko ya buƙaci a yi addua?

Radda ya ce Allah yana amsa addu’o’i, musamman a cikin watan Ramadan lokacin da al'ummar musulmi suka himmatu wajen neman samun shiriya.

Ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatinsa ta fara don inganta rayuwar al'ummar jihar.

Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na bayar da tallafi ga marasa galihu da mabuƙata a jihar.

Radda ya ce zai kuma ci gaba da bayar da alawus-alawus na wata-wata ga malaman addini da sarakunan gargajiya da ƴa ƴan jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

A kwanakin baya dai gwamnan ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi ga al'ummar jihar domin azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci, za ta dauki mataki

'Ba sulhu da ƴan bindiga' - Radda

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za tayi sulhu da ƴan bindiga ba.

Gwamnan ya yi nuni da cewa yin sulhun zai sanya ƴan bindiga su riƙa yi wa gwamnati kallon ta gaza wajen kawo ƙarshensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng