Gwamna Ya Fito Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Aka Kasa Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Gwamna Ya Fito Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Aka Kasa Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro sakamakon hare-haren ƴan bindiga
  • Gwamna Uba Sani na jihar ya yi nuni da cewa an kasa shawo kan matsalar ne saboda ƴan sa-kai ba su da makamai masu inganci
  • Ya sake yin kira da a samar da ƴan sandan jihohi ta yadda mutanen da ke zaune a ƙauyuka za su iya kare kansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan dalilan da yasa jihar ta kasa magance matsalar hare-haren ƴan bindiga.

Gwamnan ya yi nuni da cewa an kasa shawo kan matsalar ne saboda ƴan sa-kai ba su da ingantattun makamai, cewar rahoton jaridar PM News.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan 'yan bindiga sun hallaka babban malamin addini a wani sabon hari

Uba Sani ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamna Uba Sani ya koka kan matsalar rashin tsaro Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ƴan sa-kai ba za su iya riƙe abin da ya wuce ƴan ƙananan bindigu ba, amma waɗannan ƴan bindigan suna zuwa ne ɗauke da AK-47 da mugayen makamai. Wannan shi ne halin da muka tsinci kan mu a ciki."

Wace mafita Uba Sani ya kawo?

Gwamnan ya sake yin kira kan muhimmancin samar da ƴan sandan jihohi domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, rahoton da jaridar The Nation ya tabbatar.

Uba ya yi nuni da cewa samar da ƴan sandan jihohin zai ba mutanen ƙauyuka, damar riƙe makaman da za su kare kansu da su.

"Wannnan shi ne dalilin da ya sa wasu daga cikinmu suka dage cewa muna bukatar a samar da ƴan sandan jihohi.
"Idan aka samar da ƴan sandan jihohi, za a ba su dama bisa dokar kundin tsarin mulki su riƙe makamai ciki har da AK-47. Daga nan waɗannan ƙauyukan za su iya kare kansu.

Kara karanta wannan

Sace-sace a Kaduna da Borno: An ba Shugaba Tinubu mafita

"Amma har zuwa wannan lokacin, ƴan sa-kai za su iya aiki ne kawai tare da sojoji. Za su iya aiki ne kawai tare da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen samar musu da bayanan sirri."

- Uba Sani

'Yan bindiga sun sace mutanen Kaduna 87

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon hari a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Ƙaduna.

A yayin harin, ƴan bindigan sun sace mutum 87 tare fasa shaguna inda suka kwashi kayan abinci da sauran kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng