An Shiga Jimami Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Malamin Addini

An Shiga Jimami Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Malamin Addini

  • Wasu ƴan bindiga sun kashe wani shugaban babbar coci da wani Fasto a ƙaramar hukumar Abak da ke jihar Akwa Ibom
  • An tattaro cewa ƴan bindigan sun mamaye harabar cocin ne a kan babura a yayin wani taron cocin a ƙarshen mako
  • Wani shugaban al’ummar yankin, Bishop John Jeremiah Kpongkpong, ya ce ya sanar da ƴan sanda wannan mummunan lamari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom - Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kashe wanda ya kafa cocin Mount of Solution Redeemed Church (MSRC), Apostle Elisha Asuquo a Ikot Ekang, ƙaramar hukumar Abak ta jihar Akwa Ibom.

Mummunan lamarin ya faru ne bayan da ƴan bindigan suka kai hari a hedikwatar cocin da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a ƙarshen makon jiya.

Kara karanta wannan

FCT: An tafka ɓarna yayin da mutane ke tsaka da sallar tarawihi a watan azumin Ramadan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Akwa Ibom
'Yan bindiga sun kashe babban fasto a jihar Akwa Ibom Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Maharan sun kuma harbe faston da ke kula da cocin, Aniekan Ibanga a yayin da suka tarwatsa taron cocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka halaka mutanen

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, wani mazaunin garin ya ce maharan sun aukawa harabar cocin ne a kan babura, inda suka tsere ta babbar hanyar Abak-Ikot Ekpene.

A cewar majiyoyi daga cocin, Apostle Asuquo yana gudanar da sulhu ne a tsakanin wata mata da mijinta da suka rabu kafin aukuwar mummunan lamarin, rahoton Newsdirect ya tabbatar.

Wani shugaban al’umma a Ikot Ekang, Bishop John Jeremiah Kpongkpong, ya ce irin wannan mummunan lamari bai taɓa aukuwa a garin ba.

A kalamansa:

“Da misalin karfe 8 na dare, ina halartar wani taro a coci, sai wani ya kira ni ya tambaye ni ko na ji an harbe Apostle Elisha da Fasto Aniekan.

Kara karanta wannan

Ana cikin azumi 'yan ta'adda sun kai mummunan hari a jihar Arewa

"Ina cikin wayar kuma sai wani ya shigo ya fada mani cewa an kashe Apostle Elisha da Fasto Aniekan.
"Dole ne na bar wajen na garzaya zuwa fadar Hakimi domin in sanar da shi abin da ke faruwa. Bayan na sanar da hakimin, sai ya umarce ni da in kira ƴan sanda, wanda na yi hakan.
"Lokacin da na isa harabar cocin, na ga mutane da yawa suna taru yayin da ƴan sanda daga Abak ke gudanar da ayyukansu."

Ƴan sanda sun mayar da martani

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom, CSP Odiko MacDon, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don cafko waɗanda suka aikata ɗanyen aikin.

Ƴan bindiga sun hallaka basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa Yan bindiga sun hallaka basaraken Riruwai a ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon lokaci.

Marigayin mai suna Alhaji Garba Badamasi ya gamu da tsautsayin ne a ranar 15 ga watan Maris bayan maharan sun kai farmaki a garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng