An Yi Ta'adi Bayan An Kai Harin Kunar Bakin Wake a Borno, Bayanai Sun Fito

An Yi Ta'adi Bayan An Kai Harin Kunar Bakin Wake a Borno, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta tabbatar da cewa an kao harin ƙunar baƙin wake a ƙaramar hukumar Biu ta jihar
  • Harin dai an kai shi ne da misalin ƙarfe 8:00 lokacin da al'ummar musulmi suke gudanar da sallar dare
  • A yayin harin, ɗan ƙunar baƙin waken wanda ya doshi wani masallaci ya salwantar da ransa tare da jikkata wasu mutum biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar ƴan sandan jihar Borno a ranar Litinin, 18 ga watan Maris, ta tabbatar da cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a jihar.

Harin ƙunar baƙin waken dai an kai shi ne a ƙaramar hukumar Biu ta jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan 'yan bindiga sun hallaka babban malamin addini a wani sabon hari

An kai harin kunar bakin wake a Borno
Mutum biyu sun jikkata a harin kunar bakin-wake a Borno Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Daso Nahum, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin, ga manema labarai, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku a Borno

Nahum ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, a lokacin da al'ummar musulmi a garin ke gudanar da sallar dare.

A kalamansa:

"Ɗan ƙunar baƙin waken da ake zargin yana kan hanyar zuwa masallaci ne ya tayar da bam ɗin a kusa da wani shatale-tale, inda ya salwantar da ransa.
"An garzaya da wasu mutum biyu waɗanda bam ɗin ya raunata lokacin da suke wucewa zuwa asibiti domin yi musu magani.
"Nan da nan aka tura tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru domin tabbatar da tsaro".

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

Wane kira ƴan sandan Borno suka yi?

Kakakin ya buƙaci jama’a da su ƙara taka tsan-tsan, musamman a wannan lokaci na Ramadan da mafi akasarin al'ummar musulmi ke gudanar da sallolin dare.

A cewarsa:

"Ya kamata jama’a su tabbatar sun ƙara tsan-tsan kuma ka da su yi ƙasa a gwiwa wajen kai rahoton duk wani abin da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro."

Ƴan ta'adda sun sace mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan ta'adda sun kai sabon hari a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A yayin harin da aka kai cikin tsakar dare, ƴan ta'addan sun yi awon gaba da mutum 87 tare da sace kayan abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel