Ka Bude Iyakar Jamhuriyar Benin da Najeriya, Basarake a Osun Ya Roki Tinubu Alfarma

Ka Bude Iyakar Jamhuriyar Benin da Najeriya, Basarake a Osun Ya Roki Tinubu Alfarma

  • Basarake daga jihar Osun ya ba shugaban kasa shawari kan tattalin arzikin Najeriya da kuma wahalhalun da ake ciki
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan kasa ke ci gaba da kuka kan yadda tattalin arzikin kasar ke lalacewa
  • Ya zuwa yanzu, an shawarci Tinubu ya bude iyakar Najeriya da Benin don habaka tattalin arziki mai karfi

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Osun - Basarake Oba Hameed Oyelude, Olowu na Kuta a karamar hukumar Ayedire ta Osun, ya roki shugaba Bola Tinubu da ya bude kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.

Oba Oyelude, ya yi wannan roko ne a wata tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Lahadi a fadarsa da ke Kuta, inda ya ce bude kan iyakar zai sauwaka wa ‘yan Najeriya a matsalolin tattalin arziki da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

Kwastma ta sake bude iyaka mai muhimmanci a yankin Arewa bayan umarnin Tinubu, akwai bayanai

An ba Tinubu shawarin bude iyakar kasa
An ba Tinubu shawarin ya bude iyakar Najeriya da Benin | Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Dalilin garkame iyakar Najeriya da Benin

Da yake jawabi, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A lokacin da aka rufe iyakar Jamhuriyar Benin, gwamnatin tarayya na kokarin kare tattalin arzikin kasar ne.
"Amma ina so na roki shugaban kasa ya duba yiwuwar sake bude kan iyakar don rage radadin da 'yan Najeriya ke ciki."

Ku yi hakur, Oba ga 'yan Najeriya

Oba Oyelude ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasa, yana mai cewa Tinubu na da nufin alheri ga kasar ta hanyar cire tallafin man fetur, rahoton Daily Trust.

Ya kara da cewa:

“Ribar cire tallafin man fetur na zuwa, amma watakila ba nan kusa ba. Don haka ya kamata mu yi hakuri da shugaban kasa.
“Ya kamata mu baiwa wannan gwamnatin lokaci. Ba shakka za mu isa wurin.”

Kada ka dauki shawarin IMF, Oba ga Tinubu

Kara karanta wannan

Yayin da ake cikin wani hali, Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya, bayani sun fito

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da kada ta dauki wani wasu shawarwari da manufofin Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), Daily Post ta tattaro.

Oba Oyelude ya ce duk da cewa babu laifi wajen duba ga shawarwarin IMF, amma ya zama dole a yi hakan ta hanyar da za ta dace da kasar.

An umarci bude iyakar Najeriya da Nijar

A wani labarin, kwanturola Janar ta hukumar shige da fice ta kasa, Kemi Nanna Nandap, ta umurci dukkan shugabannin hukumar da su yi gaggawar bin umarnin Shugaba Bola Tinubu na bude iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Ga masu ruwa da tsaki a ayyukan hukumar, Nandap ta kuma ba su tabbacin bin matakan da suka dace yayin shige da fice a iyakokin kasashen biyu.

Idan baku manta ba, Tinubu ya ba da umarnin bude iyakar tun bayan da aka gama daidaita abubuwa kan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.