Kwastma Ta Sake Bude Iyaka Mai Muhimmanci a Yankin Arewa Bayan Umarnin Tinubu, Akwai Bayanai
- Yayin da hukumar Kwastam ke bin umarnin Shugaba Tinubu, ta sake bude iyakar Kamba a jihar Kebbi
- Kwanturolan Kwastam a jihar, Iheanacho Ojike ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan umarnin Shugaba Tinubu
- Ojike ya ce an bude iyakokin ne domin ci gaba da halastattun kasuwanci da za su kawo ci gaba a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Hukumar Kwastam reshen jihar Kebbi ta sake bude iyakar Najeriya da ke Kamba a jihar da ke Arewacin Najeriya.
Kwanturolan hukumar a jihar, Iheanacho Ojike shi ya tabbatar da haka a kokarin bin umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Yaushe aka bude iyakar a jihar Kebbi?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Tajudden Salisu ya fitar a jiya Asabar 16 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jim kadan bayan bude iyakar a gaban dagacin Kamba, Alhaji Mamuda Fana, Ojike ya ce wannan iyaka ta na da matukar tasiri a samun kudin shiga ga jihar Kebbi.
Ya ce ana ci gaba da bude iyakokin ne domin yin kasuwanci halastattu ba tare da matsala ba, cewar Channels TV.
Gargadin hukumar kan fitar da kaya waje
Ya kuma ce za su yi duk mai yiyuwa domin ganin sun dakile shigo da makamai da sauran abubuwa marasa amfani daga iyakokin.
Kwanturolan ya kuma ce fitar da kayan hatsi kasashen ketare ya haramta ganin yadda ake fama da karancin abinci a kasar.
Da ya ke martani, Mallam Fana ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan wannan mataki da ta ke dauka kan iyakokin, cewar FRCN.
Dagacin ya kuma ce zai taimaka wurin tabbatar da yin halastattun kasuwanci ganin yadda 'yan kauyen suka saba da kasuwancin a bakin iyakokin.
Tinubu ya bude iyakoki
A baya, mun ruwaito muku cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin da ke tsakanin Najeriya da Nijar.
Iyakokin da matakin ya shafa su ne na sama da kuma kan tudu wanda zai taimaka wurin tabbatar da harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen.
Wannan na zuwa ne bayan kiraye-kiraye da ake ta yi ga shugaban domin samun sauƙin kayayyakin masarufi a kasar.
Asali: Legit.ng