Da Gaske Ne Aisha Buhari Ta Ce Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Rasu a 2017? Ga Gaskiya
- An yada jita-jita da yawa a kafafen sada zumunta cewa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a 2017
- Buhari ne shugaban kasa na 15 kuma wanda ya mulki Najeriya a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023 kafin Tinubu
- An binciko gaskiyar lamari game da jita-jitan da ke yawo cewa matar Buhari ta alanta mutuwarsa a wancan lokacin
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Daura, jihar Katsina - Jita-jita ta yada gari, musamman a kafafen sada zumunta cewa, Aisha Buhari ta ce mijinta tsohon shugaban kasa Buhari ya rasu a 2017.
Jita-jitar ta kuma yi bayanin cewa, ai mutumin da ake gani bayan 2017 a matsayin Buhari ba shi bane, wani daban ne da ke kwaikwayarsa.
Jita-jitar dai ta fito ne daga mujallar Igbo Times, inda ta ce Aisha ta amsa cewa, mijinta ya rasu a 2017 a birnin Landan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda batun faro a shekarun baya
Mujallar ta naqalto Aisha na cewa, wani dan kasar Sudan aka dauko domin maye gurbin Buhari, wanda kuma aka yi sa'an suna kama ta fuska da dabi'a.
A cewar mujallar, Aisha ce tace:
"Mijina Buhar ya rasu a 2017 a kasar Burtaniya kafin daga bisani wani mutumin Sudan da aka biya ya fara kwaikwayarsa kuma ya fara dabi'u irin na marigayin mijina."
An bankado gaskiya, Buhari bai mutu ba
Legit a tun farko ta rahoto yadda kafafen sada zumunta suka cika da karairayin yadda wani wani dan Sudan mai suna Jubril ya maye gurbin Buhari.
A binciken da AFP Fact Check ta yi, jita-jitar ta fara ne tun 2017 kuma ta yadu a kafafen Facebook, Twitter da ma kafar YouTube.
'Yan awaren Biafra ne suka fara yayata labarin kasacewar a tun farko sukan bayyana kiyayya ga tsohon shugaban kasar.
Labari ne na karya, bincike ya tabbatar
A wani rahoton da aka buga a ranar Juma'a 23 ga watan Faburairu, Africa Check ta bayyana cewa, rahotannin mutuwar Buhari a 2019 da 2020 duk karya ne.
Africa Check ta ce:
"Babu wata hujja da ke nuna cewa Buhari ya mutu a lokacin da yake mulki kuma wai har an maye gurbinsa da mai kama dashi.
"Duba da mummunan yaduwar da jita-jitar ta yi, da matar tsohon shugaban kasar za ta fito ta yi bayanin mutuwar mijinta a 2017 a kafafen sada zumunta na gida da na waje.
"Sai dai, babu wata kafa ta gida ko ta kasa da kasa da ta taba rahoto bayaninta.
"Batun dai ya yadu ne a kafafen sada zumunta a 2017. Har yanzu yana ci gaba da yaduwa a 2024."
Femi Adesina ya karya 'yan Biafra
A tun farko, mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ya taba karyata wannan batu da ake cewa Buhari ya mutu.
Ya bayyana cewa, hankali ma ba zai dauka ba ace shugaban kasa guda ya mutu har a maye gurbinsa da na bogi.
A wancan lokacin, mutane da yawa sun yi imani da cewa, da gaske shugaban kasar ya kwanta dama.
Asali: Legit.ng