Kar kan ku ya kulle: Buharin ne shugaban ƙasa ba Jubril Sudan ba; Femi Adesina ya yi raddi

Kar kan ku ya kulle: Buharin ne shugaban ƙasa ba Jubril Sudan ba; Femi Adesina ya yi raddi

- An dade ana rade-radin cewa wai an musanya shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da wani Jubril daga Sudan

- Masu irin zargi na kafa hujja da cewa Buhari ya rasu a wata doguwar jinya da ya yi a 2017 amma sai aka rufe

- Femi Adesina ya ce yana matukar mamakin yadda kan mutane yake kullewa har suke yarda da wannan shashanci

Mai bada shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaba Buhari, Femi Adesina, ya ga baiken Shugaban ƙungiyar ƴan asalin Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, akan cewar wai mutumin da ke zaune a fadar shugaban ƙasa ba Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bane, Jubril ne daga Sudan.

Adesina a cikin wani rubutu da ya wallafa mai taken; Buhari a shekaru 78: Idan da munsan wannan shugaban ƙasar, to da yabonsa zamu ke yi, inda ya dage kan cewa Buhari yana nan garau kuma lafiya ƙalau.

Kanu yayi iƙirarin cewa mutumin da ke fadar shugaban ƙasa ba Buhari bane, ɓattabaminsa ne kurum. Ya kuma kawo wasu hotuna a matsayin hujja don tabbatar da iƙirarinsa, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

KARANTA: FG: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji tallafin biliyan N12.55

Da yake maida martani, Adesina ya yi tirr da iƙirarin da kuma ƙaryata hakan, inda ya bayyana labarin nasa a matsayin shashanci da abin baƙin ciki wasu masu hankali suka fara yarda.

Kar kan ku ya kulle: Buharin ne shugaban ƙasa ba Jubril daga Sudan ba; Femi Adesina ya yi raddi
Kar kan ku ya kulle: Buharin ne shugaban ƙasa ba Jubril daga Sudan ba; Femi Adesina ya yi raddi @Bashir Ahmad
Source: Facebook

Adesina a kalamansa ya ce; "wannan ba Jubril bane daga Sudan, kuma ba Muhammad Buhari da wasu mutane ke faɗin ya kwanta dama a jinyar da yayi ta shekarar 2017 bane.

"Idan akwai wanda kuke ganin akwai ɓaddabami a fadar shugaban ƙasa to ba dai Buhari. Wannan tsabagen shashanci ne,wanda abin baƙinciki ne ace masu hankali da tunani sun yarda.

KARANTA: Kaduna: El-Rufa'i ya bayar da umarnin rufe wuraren taron biki da gidajen rawar disko

"Bari na baka labari. A ranar da Shugaban ƙasa ya dawo a watan Agusta na 2017, bayan watanni baya nan, Shugaban rundunar tsaro, Gen Abayomi Olonisakin, yana aurar da ɗiyarsa ranar."

"Na halarci bikin a coci, cikin irin shigar babbar riga (Agbada) da hula wadda ta yi dai dai da kayan. Daga wurin kaitsaye na wuce filin jirgi don tarbar shugaban ƙasa a wata liyafa da aka haɗa."

"Muka shiga jerin masu sannu da zuwa kamar yadda muka saba. Shugaban ya ringa bi yana gaisawa da mu yana girgiza kansa kuma ya na zolayarmu ɗaya bayan ɗaya. Da ya zo kaina, muna gaisawa sai yace; Adesina, wannan sune kaya mafi kyawu da na taɓa gani ka sanya."

"Sai dukkaninmu muka yi dariya har masu hoto suka yi ta ɗauka. Ina tuna cewar mutane da yawa sun tambayeni dalilin da ya sa muka ƙyaƙyata dariya haka da ni da shugaban ƙasa."

"Ta yaya Jubril daga Sudan zai gane ni a matsayin Adesina? Ta ina zai san bana saka babbar riga har ya yi magana akai? Ya aka yi kan wasu mutane ya ke kullewa ne?.

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Sanatoci sun koka akan gazawar shugaba Buhari wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fama da ita.

Sun kuma tunawa Shugaban ƙasar irin ƙarfin ikon da doka ta basu na tsige Shugaban ƙasa kamar yadda yake a kundin dokokin Najeriya.

Sanatoci sun yi niyyar ɗaukar ƙwararan matakai da suka haɗar da dakatar da kasafin kuɗin 2021, wanda hakan zai tilastawa shugaban ƙasa aiwatar da ƙudirinsu da gaske.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel