Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Fitaccen Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Rasu a Watan Ramadan
- Sarkin ƙasar Ibadan, Olubadan na Ibadanland, Oba Lekan Balogun, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 82 a duniya
- Gwamma Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce mai martaba sarkin ya koma ga Mahaliccinsa ranar Alhamis a asibitin jami'ar UCH
- Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, masarautar Ibadanlanda, majalisar sarakunan Oyo da sauran al'umma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Fitaccen sarkin ƙasar Ibadan, Olubadan na Ibadanland, Oba Lekan Balogun, ya riga mu gidan gaskiya. Sarkin na 42 a tarihi ya rasu ne yana da shekaru 82.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ne ya tabbatar da wannan rasuwar a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Sulaimon Olanrewaju, ya fitar ranar Alhamis.
Makinde ya bayyana cewa basaraken ya rasu a asibitin jami'a (UCH) ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi Oba Balogun ya shafe shekaru biyu ne kadai a kan karagar mulki, an naɗa shi Sarki kuma Gwamna Makinde ya mika masa sandar mulki ranar 11 ga watan Maris, 2022.
Gwamna Makinde ya miƙa ta'aziyyar Olubadan
"Tare da mika wuya ga ikon Allah, ina mai sanar da rasuwar mahaifinmu, Mai Martaba Sarki, Oba Balogun Alli Okunmade II, Olubadan na 42 na Ibadanland.
"Ibadanland ta samu babban ƙwararren Olubadan, wanda ya yi kafa tarihi da ba za a taɓa mantawa da shi ba kuma ya samu nasara sosai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
"A madadin gwamnati da al'ummar Oyo, ina miƙa ta'aziyya ga iyalan Oba Balogun, masarautar Olubadan, majalisar sarakuna ta jiha da al'ummar Ibadanland."
- Seyi Makinde.
Gwamna Makinde ya ƙara da cewa rasuwar Dakta Balogun ta kawo ƙarshen zamaninsa a karagar mulki kuma ya bar babban giɓi a tarihin masarautar da al'adunta.
Marigayi Olubadan bai jima a mulki ba
Punch ta tattaro cewa an haifi marigayi Olubadan a ranar 18 ga watan Oktoba, 1942 kuma ya gaji sarauta shekaru biyu da suka wuce bayan mutuwar Oba Saliu Adetunji.
A ranar litinin, marigayi sarkin ya yi bikin cika shekaru biyu a gadon mulki, inda ya gode Allah bisa baiwar da ya yi masa.
Basaraken ya godewa masu ba shi shawara kan irin goyon bayan da suka ba shi zuwa yanzu.
Tsadar rayuwa: Basarake ya gano mafita
A wani rahoton kuma Oba na Iwoland, Abdulrosheed Akanbi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya samar da hukumar kayyade farashin kaya a kasar.
Akanbi ya ce wannan mataki ne kadai zai dakile hauhawan farashin da wasu masu hadama ke yi a duk lokacin da suka ga dama.
Asali: Legit.ng