Kotu Ta Garƙame Makusancin Gwamnan PDP a Gidan Yari Kan Zargin Ta'addanci da Kisan Rayuka

Kotu Ta Garƙame Makusancin Gwamnan PDP a Gidan Yari Kan Zargin Ta'addanci da Kisan Rayuka

  • Babbar kotun tarayya ta fara sauraron karar da aka gurfanar da hadimin gwamnan jihar Osun kan tuhume-tuhume 10
  • Alkalin kotun ya umarci a tsare Mista Olalekan Oyeyemi a gidan yarin Ile-Ife har zuwa zama na gaba wanda za a yanke hukunci kan bukatar beli
  • Hukumar ƴan sanda ta gurfanar da makusancin gwamnan a gaban ƙuliya kan zargin ta'addanci da kisan rayukan mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Kotu ta umarci a tsare makusancin Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, Olalekan Oyeyemi, a gidan gyaran hali kan zargin ta'addanci da kisan kai.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kotun ta umarci a garƙame hadimin gwamnan a kurkukun Ile-Ife bisa tuhumar da ta shafi ta'addanci da kisan mutum huɗu.

Kara karanta wannan

Buga takardun bogi: Kotu ta dauki mataki kan tsohon shugaban bankin NIRSAL, Abdulhameed

Gwamna Adeleke na jihar Osun.
Hadimin gwamna zai yi zaman gidan kurkuku Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Gwamna Adeleke ya nada Olalekan wanda aka fi sani da ‘Sarki’ a matsayin mamban kwamitin ladabtarwa na hukumar sufurin jihar Osun jim kadan bayan rantsar da shi a 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi ake tuhumar makusancin gwamnan?

An gurfanar da shi ne a babbar kotun tarayya da ke zama a Osogbo, jihar Osun bisa tuhume-tuhume 10 da suka hada da ta’addanci da kuma kisan kai.

Ɗan sanda mai shigar da kara, Umar Rabiu ya bayyana cewa Olalekan ya aikata laifukan ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 22 ga watan Agusta da 28 ga Nuwamba, 2022 a Osogbo, babban birnin Osun.

Ya ce:

"Olalekan ya hada baki da wasu wajen aikata ta’addanci ta hanyar amfani da bindigogi, ya farmaki magoya bayan All Progressives Congress (APC) da sauran mazauna Orita CMS da ke Ayepe da Ayetoro a Osogbo.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamnan APC zai rage farashin kayan abinci da 25% yayin da aka fara azumi

"Ya jagoranci kashe mutum huɗu da suka haɗa da Muraina Olayiwole, Tope, Tajudeen Rabiu da kuma Oyewale Sharif."

Rabiu ya ƙara da cewa laifukan sun ci karo da sashe na 26(1)(a), 2(2), i, h, na dokar ta'addanci 2022, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Lauyan hadimin gwamnan ya nemi beli

Sai dai Olalekan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su yayin da lauyansa, Edmund Biriomoni ya shigar da bukatar neman beli.

Mai gabatar da kara daga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Rabi’u ya ce zai bukaci karin lokaci don mayar da martani kan buƙatar beli da lauyan wanda ake ƙara ya gabatar.

Alkalin kotun, Mai shari’a Emmanuel Ayoola ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a gidan yari na Ile-Ife, sannan ya ɗage zaman zuwa ranar 19 ga watan Maris.

Gwamna Makinde ya fara rusau a jihar Oyo

A wani rahoton kuma Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya fara rusau a Ibadan, babban birnin jihar inda aka fara zargin ya rushe gidaje masu ɗinbin yawa.

Rahoto ya nuna rusau zai shafi kauyuka 12 da ke kusa da titin Circular a ƙaramar hukumar Ona Ara ta jihar, amma wani shugaban al'umma ya koka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262