Ramadan: Shugaba Tinubu Ya Halarci Buɗe Tafseer Na Alƙur'ani, Ya Aika Saƙo Ga Musulmin Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ya halarci buɗe tafsirin alƙur'ani mai girma na watan Ramadan wanda aka saba yi a gidan gwamnati
- Shugaba Tinubu ya jagoranci buɗe tafsirin, inda ya buƙaci Musulmi su yi amfani da damar azumi wajen yi wa ƙasa addu'a
- Babban limamin fadar shugaban kasa, AbdulWaheed Suleiman, ya yi addu'ar Allah ya dafa wa Tinubu a kokarinsa na sauke nauyin da ke kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ɗaukacin mabiya addinin Musulunci a ƙasar nan su yi amfani da wannan damar wajen yi wa Najeriya addu'ar ci gaba.
Shugaba Tinubu ya shawarci Musulmai su sanya ƙasa cikin addu'o'insu a wannan wata mai tarin albarka domin samun ci gaba a Najeriya, Daily Trust ta rahoto.
Tinubu ya halarci buɗe tafsirin Alƙur'ani
Bola Tinubu ya yi wannan jan hankali ne yayin da yake buɗe tafsirin Alqur'ani mai girma na shekara-shekara da aka saba yi a fadar shugaban ƙasa ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa Tinubu ya godewa Allah SWT bisa yadda ya tausaya wa kasar nan ta wuce wasu matakai a baya, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
“Muna godiya ga Allah da ya bamu ikon ganin watan Ramadan, Muna ƙara gode wa Allah da ya sa muka gama zaɓe kuma ya yi mu ’yan Najeriya.
"Allah ya bamu ƙarfi da rayuwa har mu ga karshen watan Ramadan, kuma mu ci gaba da bauta Masa. Ina shawartarku da ku ci gaba da sanya kasar nan cikin addu'a."
- Bola Tinubu.
Ya kuma roki Allah Mai Girma da Ɗaukaka ya sake kawo wa Najeriya ɗauki domin ta iya shawo kan ƙalubalen tsadar rayuwa da matsin tattalin arzikin da take ciki.
Tinubu ya yi kira ga masu hannu da shuni su tausaya kuma su taimaka wa masu karamin karfi a cikin al’umma yayin da Musulmi ke ci gaba da gudanar da ayyukan ibada a cikin watan Ramadan.
An yi wa Tinubu addu'ar samun nasara
Babban limamin masallacin gidan gwamnati, Malam AbdulWaheed Suleiman, ya roƙi Allah ya ci gaba da taimakawa Tinubu a kokarinsa na jagorantar kasar nan zuwa tudun mun tsira.
Ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2024 Musulmai suka fara azumin farko a watan Ramadan bayan sanarwan mai alfarma sarkin Musulmi.
Tinubu ya naɗa tsohon shugaban PDP a muƙami
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mista Felix Amaechi Obuah a matsayin shugaban hukumar AMMC.
Mista Obuah shi ne tsohon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa, PDP a reshen jihar Ribas wanda ya gabata.
Asali: Legit.ng