Gwamnatin Tinubu Ta Gano Shirin Ƴan Bindiga Na Kai Hare-Hare Makarantu a Jihohi 14, Ta Faɗi Sunaye
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bankaɗo wani tuggu na yiwuwar ƴan bindiga su kai hari makaranru a jihohi 14 a Najeriya
- Hajia Halima Iliya, jagorar shirin samar da kuɗaɗen tsaron makarantu a Najeriya ta ce gwamnati na ƙara tsaurara matakan tsaro a jihohin da abin ya shafa
- Kwamandan sashin tsaron makarantu na hukumar Sibil Difens ta kasa (NSCDC), Hammed Abodunrin, ya lissafo jerin jihohin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta ce jihohi 14 da birnin tarayya Abuja na cikin haɗari game da hare-haren ƴan bindiga
Gwamnati ta bayyana cewa ta gano cewa gungun ƴan bindiga da ƴan ta'adda na ƙulle-kullen kai sababbin hare-hare makarantu a waɗannan jihohi 14 da kuma birnin Abuja.
Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane a Abuja da wasu jihohi musamman a Arewa maso Yammacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane jihiho ne ƴan bindiga ke shirin kai hari?
Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, shugabar shirin samar da kuɗin tsaron makarantu a Najeriya, Hajia Halima Iliya, ce ta ankarar da haɗarin da jihohin ke ciki ranar Lahadi.
Ta ƙara da cewa tuni aka tattara bayanan dukkan makarantun da ke fuskantar haɗarin harin ƴan bindigan domin ɗaukar matakai tun da wuri-wuri.
Sai dai Halima ta ƙi ambatar sunayen jihohin amma kwamandan cibiyar sa ido kan tsaron makarantu ta hukumar Sibil Defens, Hammed Abodunrin, ya jero sunayen jihohin.
Rahoton Bussiness Day ya tattaro sunayen jihohin, sun haɗa da.
1. Jihar Adamawa
2. Jihar Bauchi
3. Jihar Borno
4. Jihar Yobe
5. Jihar Benuwai
6. Jihar Katsina
7. FCT, Abuja
8. Jihar Kebbi
9. Jihar Sakkwato
10. Jihar Filato
11. Jihar Zamfara da wasu jihohi guda uku.
Akalla dalibai, malamai, da mata ƴan gudun hijira 465 aka sace a makon da ya gabata kuma har yanzu suna hannun wadanda suka yi garkuwa da su, Daily Trust ta tattaro.
Ramadan: Katsina zata raba kayan abinci kyauta
A wani rahoton na daban Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya kaddamar da kwamitin da zai jagoranci ciyar da talakawa marasa galihu sama da miliyan biyu a Katsina
Gwamnan ya bayyana cewa shirin zai tallafawa kimanin mutane 72,000 a kowace rana tun daga farkon Ramadan zuwa karshe
Asali: Legit.ng