Ramadan 2024: Muslman Najeriya Na Zuba Ido Kan Ganin Jaririn Watan Ramadana
- Ana ci gaba da jiran ganin watan Ramadana ko sabanin haka a Najeriya, yayin da aka gani a wasu kasashen duniya
- Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jaririn watan Ramadana, za a fara Azumi a ranar Litin 11 ga watan Maris
- Ya zuwa yanzu dai, hukumomin ganin wata a Najeriya daga fadar sarkin Musulmi sun ce a ci gaba da duban watan mai alfarma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwa
Najeriya - Al’ummar Najeriya da sauran kasashen duniya na ci gaba da zuba ido kan ganin watan Ramadana domin fara ibada mafi girma a wurin Musulmai.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da shiri da sanya ido a kasar domin samun rahotannin da ke bayyana ganin watan ko akasin hakan.
A lissafin wata, yau ne 29 ga watan Sha’aban, wacce ke zuwa gabanin Ramadana da ake Azumin kwanaki 29 ko 30.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ake yi a watan Ramadana?
Watan Ramadana ne na tara a jerin watannin Muslunci 12, kuma a ciki ne Musulmai ke ba da himma ga aikata ayyukan ibada, musamman yawaita sallah da Azumi.
Wannan lamari ne da ke daukar hankalin duniya, domin duk Musulmi yake a duniya kan azumci wannan wata mafi shahara a addinin Islama.
Ana kwadaitar da Musulmai su kasance masu kamewa da yawaita neman gafara da rokon ni’imomin Allah a cikin watan.
An ga wata a kasar Saudiyya
A gobe Litinin 11 ga watan Maris ne za a fara Azumin watan Ramadana a kasar Saudiyya.
Wannan na zuwa ne bayan sanar da ganin watan a yammacin yau Lahadi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A wasu lokutan, akan saba tsakanin Najeriya da Saudiyya wajen daukar Azumi da kuma ajiye shi a watan Ramadana.
Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban wata
A tun farko, mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi a Najeriya su fara duba jinjirin watan Ramadan daga ranar Lahadi.
Majalisar koli ta shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA) karkashin Sarkin Musulmi ce ta nemi a fara duba watan a wata sanarwa ranar Jumu'a.
Sanarwan mai ɗauke da sa hannun Farfesa Salisu Shehu, majalisar ta nemi a fara duba jinjirin watan Ramadan ranar Lahadi wanda ya zo daidai da 29 ga watan Sha'aban, 1445H.
Asali: Legit.ng