Yara 9 Daga Cikin 102 da Aka Sace a Jihar Arewa Sun Samu Nasarar Kubucewa, Bayanai Sun Fito
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yara tara daga cikin 102 da aka sace a farkon watan Maris sun kubuta daga hannun mahara
- Shugaban SEMA a jihar ya ce sun samu labarin cewa yaran tara sun samu hanyar dawowa zuwa sansanin ‘yan gudun hijira
- Sai dai rahoton sace yaran ya jawo kace-nace inda gwamnatin jihar ta musanta labarin cewa sace yaran aka yi a cikin daji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno – Yara tara daga cikin 102 da kungiyar Boko Haram suka sace sun kubuta daga hannun ‘yan ta’adda a jihar Borno.
Yaran na daga cikin wadanda ke sansanin gudun hijira da aka sace a ranar 4 ga watan Maris yayin da suke diban itace a cikin daji.
Cece-kuce da aka yi kan sace yaran
Rahotanni sun tattaro cewa ba a ji wata magana ta neman kudin fansa ba daga maharan inda gwamnatin ta tsaya cewa yaran rasa hanyar dawowa suka yi ba sace su aka yi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta tattaro cewa an yi ta cece-kuce bayan sace yaran inda gwamnatin jihar ta yi watsi da cewa an sace su.
Majalisar Dinkin Duniya har ila yau, ta yi Allah wadai da sace kusan 200 daga sansanin gudun hijira a Borno, cewar NewsNow.
“Gaskiya ba mu yarda an sace yaran ba kawai dai sun rasa hanyar dawowa gida ne, idan da an sace su da zuwa yanzu maharan da sun kira domin neman kudin fansa amma ba su yi ba.”
- Shugaban NEMA, Barkindo Saidu
Martanin shugaban SEMA a jihar
Barkindo ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Ngala bayan rahoton sace yaran a ranar 8 ga watan Maris, cewar Tori News.
"Mun samu labarin cewa tara daga cikin yaran sansanin gudun hijira sun samu nasarar dawowa gida a ranar Juma'a 8 ga watan Maris."
"Bamu yadda da yawan yaran da ake yadawa an sacce ba, mu muka san yawan 'yan sansanin gudun hijirar."
- Barkindo Saidu
Mahara sun sace yaran sansanin gudun hijira
Kun ji cewa 'Yan ta'addan Boko Haram sun sace yara mata 'yan gudun hijira har 319 a jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mata da cewa an sace 'yan gudun hijiran ne a garin Ngala, hedikwatar karamar hukumar Gambarou Ngala.
Asali: Legit.ng