Gwamnan Arewa Ya Soke Nadin Babban Basarake, An Fadi Dalili

Gwamnan Arewa Ya Soke Nadin Babban Basarake, An Fadi Dalili

  • Hakimin Sauwa da ke ƙaramar hukumar Argungu a jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Tajudeen-Sauwa ya rasa muƙaminsa bayan an soke naɗin da aka yi masa
  • Gwamnatin jihar Kebbi ce dai ta soke naɗin Hakimin biyo bayan samunsa da laifin aikata rashin biyayya ga hukumomi
  • Gwamnatin ta kuma dakatar da Hakimim Guluma, Alhaji Muhammaɗ Bashir-Guluma, har na tsawon watanni shida bisa aikata irin laifin Hakimin Sauwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta soke naɗin Hakimin Sauwa, Alhaji Muhammad Tajudden-Sauwa, bisa laifin rashin yin biyayya.

Haka kuma gwamnati ta dakatar da Hakimin Guluma na tsawon watanni shida, Alhaji Muhammad Bashir-Guluma bisa irin wannan laifin, cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya maida zazzafan martani kan garkuwa da ɗalibai da ƴan gudun hijira a jihohi 2

An hukunta Hakimai biyu a Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta hukunta Hakimai biyu Hoto: Nasir Idris
Asali: Facebook

Alhaji Ahmed Idris, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kebbi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, babban birnin jihar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka hukunta Hakiman biyu?

Idris ya ce kwamitin da hukumar kula da ƙananan hukumomi ta kafa a ranar 31 ga watan Janairu, ta samu mutum biyun masu riƙe da sarautar gargajiyan da laifin rashin yin biyayya, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

An kafa kwamitin ne biyo bayan ƙorafin da ƙaramar hukumar Argungu ta yi kan Hakiman biyu.

Ya ce kwamitin ne ya ba da shawarar matakin da gwamnatin ta ɗauka wanda ya yi daidai da dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 030301(0), wacce ta shafi ayyukan rashin yin biyayya.

Idris ya ce soke naɗin da dakatar da Hakiman ta fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Fabrairun 2024.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta a sansanin ƴan bindiga a jihohin Arewa, sun kashe da yawa

Gwamna Soludo ya dakatar da basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya dakatar da Sarkin Neni, Damian Ezeani, daga kan muƙaminsa.

Gwamnan ya dakatar da basaraken ne bayan ya yi wa Sanata Ifeanyi Ubah, sanatan da ke wakiltar Anambra ta Kudu, naɗin sarauta.

Sanarwar dakatar da basaraken ta yi nuni da cewa basaraken ya karya dokar masarautun jihar Anambra da ta haramta nada mukamin sarauta ga wanda ba dan yankin masarauta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel