Ba a Gama Jimamin Kaduna Ba, 'Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jihar Arewa

Ba a Gama Jimamin Kaduna Ba, 'Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jihar Arewa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci a ƙauyen Gidan Bakuso na jihar Sokoto
  • Ƴan bindigan a yayin harin sun harbe mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu almajirai da wata mata ɗaya
  • Shugaban tsangayar ɗaliban ya tabbatar da cewa ba a ga ɗalibai 15 ba yayin da ake ci gaba ƙirga adadin yawan ɗaliban da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu almajirai da ba a tantance adadinsu ba a Gidan Bakuso da ke ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an sace ɗaliban ne daga makarantarsu da misalin ƙarfe 1:00 daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kawo babban cikas a kokarin ceto daliban da aka sace a Kaduna

'Yan bindiga sun sace dalibai a Sokoto
'Yan bindiga sun yi awon gaba da almajirai a Sokoto Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Shugaban makarantar, Liman Abubakar, ya bayyana cewa kawo yanzu ba a ji ɗuriyar dalibai 15 ba amma har yanzu suna ci gaba da ƙirgawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Abubakar, ƴan bindigan sun mamaye garin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka harbe mutum ɗaya sannan suka yi awon gaba da wata mata.

"A yayin da suke fitowa daga garin sai suka hangi ɗalibanmu suna shiga ɗakunansu da sauri, sai suka yi awon gaba da su.
"Ya zuwa yanzu mun ƙirga mutum 15 da suka ɓace kuma muna ci gaba da neman sauran."

Abubakar ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da ƴan bindiga suka kai hari a ƙauyen ba.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gada-gabas a majalisar dokokin jihar, Kabiru Dauda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta dauki hanyar ceto daliban da aka sace zuwa daji, bayanai sun fito

Ya bayyana cewa ya samu kira daga ƙauyen da misalin ƙarfe 2:00 na dare cewa ƴan bindiga sun kai farmaki.

A kalamansa:

"Na tuntuɓi shugabanni a ƙaramar hukumar da hukumomin tsaro kuma na tabbata suna yin wani abu a kai."

Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma zai tuntubi jami’in DPO na ƙaramar hukumar.

Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da jihar ke shirin ƙaddamar da rundunar jami’an tsaron al'umma, don kawo ƙarshen ƴan bindiga.

Sojoji sun gano maɓoyar ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun gano maɓoyar ƴan bindigan da suka sace ɗalibai a Kaduna.

Spjojin sun gano maɓoyar ne biyo bayan bin sahun ƴan bindigan da suka yi zuwa cikon daji bayan sun yi awon gaba da ɗaliban da malaman makarantarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng