Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya buƙaci a Fara Duba Jinjirin Watan Azumin Ramadan 1445H
- Mai alfarma sarkin musulmi a Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar na III, ya buƙaci a fara duban jinjirin watan Ramadan daga ranar Lahadi
- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da majalisar ƙoli ta shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA) ta fitar ranar Jumu'a
- Idan Allah ya sa an ga jinjirin watan a wannan rana, za a fara azumi ranar Litinin, 11 ga watan Maris, idan kuma ba a gani ba, za a fara azumi ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi a Najeriya su fara duba jinjirin watan Ramadan daga ranar Lahadi.
Majalisar koli ta shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA) karkashin Sarkin Musulmi ce ta nemi a fara duba watan a wata sanarwa ranar Jumu'a.
Sanarwan mai ɗauke da sa hannun Farfesa Salisu Shehu, majalisar ta nemi a fara duba jinjirin watan Ramadan ranar Lahadi wanda ya zo daidai da 29 ga watan Sha'aban, 1445H.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma bayyana cewa za a fara azumin watan Ramadan a ranar 11 ko 12 ga watan Maris, ya danganta da lokacin da aka ga jinjirin wata, Leadership ta ruwaito.
Majalisar shari'a NSCIA ta kuma bukaci duk wadanda suke da sahihancin ganin jinjirin watan da su sanar da mambobin kwamitin ganin wata na kasa.
"Majalisar ƙoli ta shari'ar musulunci karkashin shugabancin Sarkin musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, na taya daukacin al'umma murnar zagayowar azumin watan Ramadan na 1445H.
"Majalisar ta yi addu'ar Allah ya bai wa dukkan musulmi damar ganin wannan wata da yin ibada a cikinsa kuma tare da ribatar watan mai cike da albarka."
Yaushe za a fara duba jinjirin watan Ramadan?
NSCIA ta ƙara da cewa bayan shawarwari, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bada umarnin a fara duban jinjirin wata da zaran rana ta faɗi ranar Lahadi mai zuwa (gobe).
A ruwayar The Nation, sanarwan ta ce:
"Bisa shawarar da kwamitin ganin wata na kasa (NMSC) ya bayar, Sultan ya nemi a duba jinjirin watan Ramadan, 1445H bayan faduwar rana a ranar Lahadi 10 ga Maris 2024 wanda ya yi daidai da 29 ga Sha'aban.
“Idan musulmi suka ga jinjirin watan, mai alfarma sarkin musulmi zai bayyana ranar Litinin 11 ga Maris 2024 a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan 1445 AH.
“Idan har ba a ga jinjirin watan ba a ranar, to Talata 12 ga Maris, 2024, za ta zama farkon watan Ramadan, 1445."
Sojoji sun shirya zuwa watan Ramadan
A wani rahoton kuma Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun shirya tunkarar kowace irin barazana musamman a watan Ramadan.
A wata sanawar da DHQ ta fitar ranar Jumu'a, ta ce sojoji ba zasu yi kasa a guiwa ba sai sun ga bayan ƴan ta'adda baki ɗaya a kasar nan.
Asali: Legit.ng