“Ana Fama Har Yau”: Shehu Sani Ya Magantu Kan Maida N794,000 Mafi Karancin Albashi
- Tsohon 'dan majalisar tarayyar Najeriya, Shehu Sani, ya ce har yanzu jihohi da dama na fama da yadda za su biya ma'aikata mafi karancin albashi na N30,000
- Sani ya ce yadda za a biya mafi karancin albashi na sama da N700,000 da 'yan kwadago suka bukata wani abu ne da ya kamata a tattauna a kai
- Jaridar Legit ta rahoto cewa kungiyoyin kwadago na NLC da TUC na so a kara albashin wata da kyau domin magance halin da ake ciki na matsin rayuwa a Najeriya
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
FCT, Abuja - Shehu Sani, 'dan majalisa da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a baya, ya nuna shakku kan yiwuwar biyan mafi karancin albashi na N794,000 a Najeriya.
A wallafar da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 8 ga watan Maris, Sani ya bayyana cewa da kyar jihohi da dama ke iya biyan mafi karancin albashi na N30,000.
Jigon na PDP, ya ce ya kamata a yi muhawara kan yadda za a biya mafi karancin albashi na N700,000 da 'yan kwadago suka bukata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya rubuta:
"Da mafi karancin albashin 30k, har yanzu jihohi da dama na fama da yadda za su biya albashi. Yadda za a biya mafi karancin albashi na 700k da 'yan kwadago suka bukata abu ne da ya kamata a yi muhawara a kai.
"Buga karin takardun kudi abu ne ma da bai kamata gwamnati ta kawo tunaninsa ko a rai ba.
Kungiyar kwadago ta gabatar da bukatarta
A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto cewa kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci mafi karancin albashi N794, 000 ga ma'aikatan yankin Kudu maso Yamma.
Shugabar kungiyar a yankin, Funmi Sessi ita ta bayyana haka a yau Alhamis 7 ga watan Maris a Legas.
Ma'aikatan Akwa Ibom sun nemi N850,000
A wani labarin kuma, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun bukaci a biya ma’aikatan jihar Akwa Ibom N850,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Sunny James ne ya bayyana haka yayin taron jin ra’ayin jama’a da gwamnatin tarayya ta shirya kan mafi karancin albashi a garin Uyo, a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng