Ka Kula da Lafiyarka Madadin Yawace Yawace, Malamin Addini Ya Ba Tinubu Shawara
- Shugaba Bola Tinubu ya sake samun shawara mai kyau kan yawan tafiye-tafiye da ya ke yi daga fitaccen malamin addini a kasar
- Fasto Elijah Ayodele shi ya ba Tinubu shawara kan yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare inda ya ce ya kula da lafiyarsa yafi
- Elijah ya kuma bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da addu’a domin ganin wannan gwamnati ta samu ci gaba da zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shahararren Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya shawarci Shugaba Bola Tinubu kan yawace-yawacen da ya ke yi zuwa kasashen ketare.
Faston ya bukaci Tinubu ya tsaya kula da lafiyarsa zai fi kyau madadin yawon da yake yi da ba zai amfane shi ba, cewar Tribune.
Wace shawara Ayodele ya ba Tinubu?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Faston ya fitar inda ya ce akwai jan aiki a gaban Tinubu domin inganta Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’a domin ganin wannan gwamnati ta samu ci gaba da zaman lafiya, cewar Daily Post.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’a ga kasar da kuma Shugaba Tinubu domin ya samu lafiyar inganta kasar."
- Elijah Ayodele
...Ya bukaci Tinubu ya rika karbar shawarwari
“Shugaban ya na dauke da babban aiki wanda dole ya na bukatar addu’a domin sauke nauyin da ya ke kansa.
“Ya kamata Tinubu ya rage yawace-yawace ya roki ubangiji karin lafiya domin samun damar shawo kan matsalar da ake fama da ita a kasar.”
- Elijah Ayodele
Malamin addinin ya ce babu haske a nan gaba idan har gwamnati ba ta karbar shawarwari daga masana kan matsin tattalin arziki.
Tambuwal ya shawarci Tinubu
Kun ji cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi magana kan halin kunci da ake cki a Najeriya da tsadar rayuwa.
Tambuwal ya shawarci Tinubu da ya yi gaggawar kawo sauyi a wannan bangare musamman irin halin da ake ciki.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara gidan tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a jihar Ogun.
Asali: Legit.ng