An Kama Wasu Mata Da Suka Shahara Wajen Yankan Aljihun Fasinjoji a Abuja
- Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun kama wasu mata da suka shahara wajen yankan aljihu a babban birnin tarayya Abuja
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta kasa, Prince Olumuyiwa Adejobi, ya ce matan suna jagorantar wata kungiya ta 'one chance' kuma sun dauki mutane da yawa aiki
- Ya gargadi fasinjoji masu shiga mota a Abuja da su hankalta yayin da ya bayyana dabarun da ake amfani da shi wajen yashe mutane
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Abuja - Jami'an rundunar 'yan sanda a babban birnin tarayya, sun kama manyan masu yankan aljihu a Abuja.
Matan sun shahara wajen yiwa fasinjoji yankan aljihu yayin shiga mota ta hanyar amfani da wasu 'yan dabaru.
Wasu dabaru suke amfani da su?
Kakakin rundunar 'yan sanda, Prince Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da labarin kamun 'yan 'one chance' din a shafinsa na X a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adejobi ya kuma gargadi jama'a kan shiga motocin da ke dauke da fasinjoji uku ko hudu (yawanci maza) a baya da kuma mace a gaba.
A cewarsa, su kan tilastawa fasinja zaman gaban mota sannan su dame shi da ya matsa, har ma su karbi jakarsa da sunan taimaka masa ya zauna da kyau, daga nan sai su yashe mutum.
Haka kuma, kakakin 'yan sandan ya ce an kama daya daga cikin motocin da suka siya ta hanyar wannan aika-aika.
Ga wallafar da ya yi a shafin nasa a kasa:
A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa rundunar 'yan sanda a birnin Tarayya ta cafke wani kasurguman dan ta'adda da ya addabi jihar Nasarawa.
Wanda ake zargin, Sama'ila Wakili Fafa an cafke shi da misalin karfe 7 na yamma a dajin Sardaunan da ke jihar.
Kwamishinan rundunar 'yan sanda, Benneth Igweh shi ya bayyana haka a jiya Talata 27 ga watan Faburairu.
An kama hatsabiban 'yan bindiga
A wani labarin, jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya sun kama wasu mashahuran masu garkuwa da mutane bakwai a Abuja.
Bayan kama hatsabiban ƴan bindigan waɗanda suka shahara a garkuwa da mutane, dakarun ƴan sandan sun kwato N9m na kuɗin fansa daga hannunsu.
Asali: Legit.ng