“Ba Kullum Muke Ganin Dangote Ba”: Ma'aikatan Kamfanin Sikari Sun Magantu a Bidiyo

“Ba Kullum Muke Ganin Dangote Ba”: Ma'aikatan Kamfanin Sikari Sun Magantu a Bidiyo

  • Wasu matasa da ke aiki a kamfanin sukarin Dangote sun shiga wani gasa da ake yi a dandalin soshiya midiya cikin salo
  • 'Yan matan cikin shigarsu ta aiki da hulunan kwano sun bayyana wasu abubuwa game da rayuwarsu a matsayin masu aiki a kamfanin
  • Sun kuma yi martani ga rade-radin cewa suna ganin shugaban kamfanin, mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote, a kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wasu 'yan mata da ke aiki a kamfanin sikarin Dangote sun yi karin haske kan wasu harkokinsu a kamfanin da kuma rayuwarsu da ta yau da kullum a matsayin ma'aikata.

'Yan matan sun baje kolin hakan ne yayin da suka shiga shahararriyar gasar nan ta soshiyal midiya mai taken 'shakka babu'.

Kara karanta wannan

Dangote ya barke da kuka a wajen makokin Wigwe, ya fadi abu 1 da zai yi domin tuna marigayin

Ma'aikatan kamfanin Dangote
Ma'aikatan kamfanin Dangote sun ce ba a ganinsa a kullum Hoto: Ben Gabbe, TikTok/@big.geraldine
Asali: UGC

Kamfani sikarin Dangote na daya daga cikin kamfanonin da attajirin biloniya Alhaji Aliko Dangote ya mallaka kuma a kwanan nan ne darajarta a kasuwa ta kai naira tiriliyan 1.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin haske game da ayyukan kamfanin Dangote

A wani bidiyon TikTok, @big.geraldine, wacce ta fara aiki a kamfanin watanni uku da suka wuce kuma take aiki a sashin sarrafa sikarin, ta bayyana cewa a kullum suna kasancewa cikin rigar biri da wando da hulunan kwano.

Wata matashiyar sanye da biri da wando ta kara da cewar mutane na tunanin suna ganin Dangote a kullum, amma hakan ba gaskiya bane.

Da ta shiga gasar, wata matashiyar ma'aikaciya ta bayyana cewa suna da tikitin cin abinci duk wata.

Wata kuma cikinsu ta bayyana cewa mutane na zaton suna da kudi, amma hakan ma ba gaskiya bane. 'Yan matan sun ce suna hawa saman bene mai nisa a kullum sannan akwai motocin ma'aikata da ke daukar zuwa da dawowa daga wajen aiki.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun farmaki manoma a Borno, sun halaka mutum 3 da sace kekuna 50

Bidiyon ya kare da wata matashiya da take cewa suna samar da buhunan sikari 65, 000 a kullum.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Beyond Beauty ta ce:

"Ta yaya zan nemi aiki a Dangote???? Don Allah ki amsa mani."

Kesterblings ta ce:

"Ku ji dadin aiki."

Youngb.i.c ya ce:

"Geraldine kada ki manta da ni idan kika karbi albashi fa."

enyinwa ya ce:

"Albashi shi ne babban maganan."

obalufeiii :

"Menene dalilin da yasa sikari ya yi karanci a 'yan kwanakin nan."

Dangote ya sharbi kuka kan mutuwar Wigwe

A wani labarin, mun ji cewa an hasko Aliko Dangote yayin da ya barke da kuka a lokacin da yake ta'aziyyar marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Wigwe ya mutu ne tare da matarsa ​​da dansa, Chizoba da Chizi, a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a jihar California ta Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng