Ramadan: Sanatan Arewa Na Shirin Rabawa Mutanen Jiharsa Tirelolin Abinci 358
- Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya tanadi tireloli 358 na kayan hatsi domin talakawan Zamfara gabannin fara azumin Ramadan
- An rahoto cewa tsohon gwamnan Zamfaran zai yi rabon kayan a fadin jihar ba tare da la'akari da jam'iyyar mutum ba
- Sai dai kuma, talakawa musamman marayu da wandanda mazajensu suka mutu ne za su amfana da tallafin kayan abincin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Zamfara - Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, Abdulaziz Yari Abubakar, ya kammala shiri tsaf domin share hawayen talakawa a jiharsa.
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Yari ya tanadi tireloli 358 cike da kayan hatsi domin rabawa talakawa a lokacin azumin Ramadana.
A cikin wata sanarwa da Hon. Ibrahim Muhammad, shugaban kwmaitin yada labarai na A A Yari ya saki, ya ce kayan da za a raba a sun hada da shinkafa, gero, sikari, da masara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wanene za su ci gajiyar kayan abincin?
Muhammad ya ce za a rabawa al'ummar jihar wannan kaya ba tare da la'akari da jam'iyyar da suke yi a siyasa ba domin rage masu radadi a wata mai tsarki.
A cewarsa, tuni kaso 98 cikin dari na kayayyakin suka isa kananan hukumomi daban-daban na jihar domin wadanda za su ci gajiyar kayan tallafin su same su cikin sauki kuma a kankanin lokaci.
Ya kuma jaddada cewar dole wadanda za su amfana da wadannan kayan tallafi su kasance mabukata, musamman marayu, wadanda mazajensu suka mutu.
Daily Nigerian ta kuma rahoto cewa Muhammad ce a za a fara rabon kayan kafin ko ranar fara azumin Ramadan, sannan ya bukaci mutane da su ci gaba da yiwa tsohon gwamnan na Zamfara da kasar addu'a.
Gwamnan Kebbi zai inganta wuta saboda Ramadana
A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya ce gwamnatinsa ta fara wani yunkuri don tabbatar da ganin ta samar da wutar lantarki na awanni 24 a jihar, a lokacin azumin Ramadana.
Alhaji Idris ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan duba ayyukan da ke gudana a Birnin Kebbi, a ranar Litinin, 4 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng