Shugaban NYSC Ya Yi Shirin Toshe Hanyar da Masu Hidimtawa Kasa Ke Samun Sauki

Shugaban NYSC Ya Yi Shirin Toshe Hanyar da Masu Hidimtawa Kasa Ke Samun Sauki

  • An buƙaci matasa masu yi wa ƙasa hidima da su karɓa da zuciya ɗaya wuraren da aka tura su maimakon neman a sauya musu
  • Darakta Janar na hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Yusha'u Ahmed shi ne ya yi wannan kiran a jihar Anambra
  • Yusha'u ya buƙaci matasan da su tsaya a duk inda suka samu kansu domin bayar da irin ta su gudunmawar domin ci gaban yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Darakta Janar na hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya-Janar Yusha’u Ahmed ya buƙaci matasan da su zama cikin shirin zama duk inda suka samu kansu a ƙasar nan.

Yusha'u ya kuma gargaɗe su da su guji neman a sake musu wurin da za su yi bautar ƙasa, sai dai su zauna su bada irin ta su gudummawar don ci gaban jihohin da aka tura su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi abu 1 da za a yi wa masu neman cin hanci a gwamnatinsa

Matasa masu yi wa kasa hidima
DG Na NYSC ya bukaci matasan su zauna inda aka tura su Hoto: NYSC NDHQ
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne dai yayin da yake jawabi ga ƴan rukunin Batch '1' A yayin bikin al’adu da suka gudanar a sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima na jihar Anambra, cewar rahoton Independent.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban wanda ya je sansanin domin ziyara, ya kuma buƙaci masu yi wa ƙasa hidiman da su ɗauki tsaronsu da matuƙar muhimmanci.

Wacce shawara ya ba ƴan NYSC?

Jaridar The Nation ta ambato shi yana cewa:

"Ina buƙatar da ku mutunta ɗabi'u da al'adun mutanen wuraren da aka tura ku. Ku kasance cikin zaman lafiya da jajircewa yayin da ku ke kawo ci gaba a inda aka tura ku. Ina da tabbacin cewa za ku zaɓi ku zauna a nan bayan kun kammala.
"Hakazalika ku ɗauki tsaron ku da matuƙar muhimmanci. Mun damu da tsaron ku amma ba wanda zai kare ku fiye da kanku."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hotuna sun bayyana yayin da aka gudanar da salloli na musamman a Zaria

Fintiri Ya Gwangwaje Ƴan NYSC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana aniyarsa ta ba matasa masu yi wa ƙasa hidima alawus a duk ƙarshen wata.

Gwamnan ya yi nuni da cewa a kowane wata za a riƙa ba masu yi wa ƙasa hidimar alawus na N10,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel