Tashin Hankali: Mummunan Rikici Ya Ɓarke a Jami'ar Tarayya, An Kashe Ɗalibi Tare da Jikkata Wasu
- Sabon rikici mai alaka da ƙungiyoyin asiri ya ɓarke a jami'ar fasaha ta tarayya da ke birnin Owerri (FUTO) da safiyar ranar Jumu'a, 1 ga watan Maris
- Rahotanni sun nuna cewa an kashe ɗalibin FUTO ɗaya tare da jikkata wasu da dama yayin da suka yi faɗa da ɗaliban jami'an jihar Imo
- Legit Hausa ta fahimci cewa ɗaliban jami'ar IMSU ne suka kutsa kai cikin FUTO, lamarin da ya kawo tashin rikici a tsakaninsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Owerri, jihar Imo - Wani dalibin jami’ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) ya rasa ransa yayin da aka jikkata wasu da dama a wani lamari mai alaka da kungiyoyin asiri.
Rahoton The Nation ya nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Jumu'a yayin da wasu ɗaliban jami'ar jihar Imo (IMSU) suka shiga harabar jami'ar FUTO.
An tattaro cewa ɗaliban jami'ar IMSU sun shiga harabar gidan kwanan ɗalibai a FUTO a kan babura, lamarin da jawo suka yi arangama da juna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin faɗan da ya kaure tsakaninsu, daya daga cikin daliban jami'ar IMSU ya caka wa kwamandan tawagar Man O War na jami'ar FUTO wuƙa a wuya.
Wannan munanan raunuka da ya ji a wuyansa yayin rikicin ne ya zama ajalinsa, ya mutu nan take a wurin.
Mutuwar ɗalibin da kuma yadda aka ji wa wasu ɗalibai da dama raunuka ya jefa makarantar cikin yanayin jimami da kaɗuwa.
Matsalar tsaro a Kudu maso Gabas
FUTO na daya daga cikin manyan jami'o'in gwamnatin tarayya a Najeriya da ke da matsuguni a Imo, ɗaya daga cikin jihohin Kudu maso Gabas, inda ake fama da matsalar tsaro.
A baya-bayan nan ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da lalata kayayyakin kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) a jihar Imo. rahoton Guardian.
Yan sanda sun kama mahara 15
A wani rahoton kuma Ƴan sanda sun damƙe mutum 15 da ake zargin ƴan bindiga ne da masu hannu a aikata miyagun laifuka jihar Neja.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya ce jami'an tsaron sun kuma kwato muggan makamai da alburusai.
Asali: Legit.ng